Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Saudiya Ta Goyi Bayan Shirin Zaman Lafiya


Sarkin Saudiya Salman bin Abdulaziz
Sarkin Saudiya Salman bin Abdulaziz

Basaraken kasar Saudi Arebiya ya bayyana goyon bayansa ga shirin zaman lafiya a gabas ta tsakiya a babban taron zauren MDD a jiya Laraba, to amma bai bayyana ko Riyad za ta bi sahun Hadaddiyar Daular Larabawa wajen daidaita dantakatar ta da Isra’ila ba.

Sarki Salman bin Abdulaziz ya fada a taron da ake gudanarwa ta yanar gizo cewa, “Samar da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya shi ne babban zabin mu. Za mu iya yin komai domin aiki tare wajen cimma manufar kyautata al’amura, ta yadda zaman lafiya, kwanciyar hankali da zama tare za su wanzu a tsakanin jama’ar yankin.

“Jama’ar yankin” sun hada har da ‘yan kasar Israila, wadanda ‘yan kasar Saudiyya ba sa mu’amala da su. A makon da ya gabata Shugaban Amurka Donald Trump ya yi hasashe bayan rattaba hannu akan yarjejeniyar Abraham, wadda za ta daidaita dangantaka tsakanin Isra’ila da Daular Larabawa da Bahrain cewa, Riyadh za ta bi sahu a “lokacin da ya dace.”

To sai dai a kalaman na sa a wajen taron na MDD, Sarki Salman ya jaddada dadaddiyar matsayar Saudiyya na goyon bayan sulhu tsakanin kasashe biyu na Isra’ila da Falasdinu, tare da tabbatar da Birnin Kudus a zaman babban birnin Falsdinu mai ‘yancin kan ta.

Haka kuma ya bayyana goyon bayan shirin zaman lafiya na kasashen Larabawa na shekara ta 2002, wanda yayi tanadin tabbatar da kasar Falasdinu, a zamam sharadin daidaita dangantaka da Isra’ila.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG