Yekuwar neman zabe a Najeriya ta kan bayar da dama ga masu neman a zabesu wasu mukamai su bayyana wa jama'a kudurorinsu, ba tare da jin bukatun jama'ar ba.
Sai dai yanzu lamarin ya fara sauyawa domin wasu hukumomi da kungiyoyi kan hada ‘yan takara da jama'a wuri daya don su tattauna.
Sashen Hausa na Muryar Amurka tare da hadin gwiwar wasu jami'o'i sun shirya taron muhawarar a wasu jihohin Najeriya, inda jihar Sokoto ke daga cikinsu.
‘Yan takarar gwamna guda shida ne aka hada wuri daya, inda suka bayyana wa jama'a abin da za su yi idan suka lashe zabe a watan Maris, sun kuma yi magana akan batutuwa dabam daban kamar Ilimi, tattalin arziki, tsaro da sauransu.
Ibrahim Muhammad Liman shi ne dan takarar jam'iyyar ADP, Ahmad Aliyu Sokoto na APC, Aminu Umar Ahmad na Labour, Umar Dahiru Tambuwal na NNPP, sai kuma Sa'idu Umar dan takarar jam'iyyar PDP. Shi kuma Abubakar Umar Gada na jam'iyyar SDP.
Ba jama'a dama su yi wa ‘yan takara tambayoyi ya janyo ka-ce-na-ce, inda magoya bayan wata jam'iyya suka yi zargin cewa an bai wa wata jam'iyya dama fiye da kima.
Wasu daga cikin jama'ar da ke wurin muhawarar sun yi maraba da wannan tsarin na Muryar Amurka.
Kafin jihar Sokoto, an gudanar da irin wannan taron muhawarar a jihar Filato.
Saurari rahoton Muhamad Nasir: