Yayin da yake jawabi a wurin jana'izar sarkin Gwoza Alhaji Shehu Idris Timta a garin Gwoza, gwamnan jihar Borno Ibrahim Kashim Shettima ya kwatanta kisan da zalunci da jahilci.
An yi jana'izar cikin matakan tsatstsauran tsaro kuma an binne sarkin cikin masarautar. Gwamnan jihar ya bayyana marigayin a zaman uba kuma wani mutum mai neman zaman lafiya mai kuma hakuri. Gwamnan yace kafin 'yan bindigan su kashe sarkin sun je gonarsa sun kwashe komi kana suka sakawa gonar wuta.
Sanata Ali Ndume dan asalin garin Gwoza yace sarkin shi ne babbar inuwar da suke zama a karkashi. Duk cikin barazanar da suke fuskanta sarkin yana karfafa jama'arsa. Gashi yanzu babu shi. Ya kira mutanen garin da su hada kansu Allah kuma zai karesu.
Wani dake cikin tawagar sarkin ya bayyana yadda lamarin ya faru. Yace wata mota irin ta sarakunan ta wucesu sai mutanen dake cikinta suka fara harbi. Direban motar dake dauke da sarakunan uku ya razana sai sarkin Asikra ya fita ya shiga wata motar. Sarkin Uba ma ya fita ya fara gudu lamarin da yasa an bar sarkin Gwoza shi kadai cikin motar. Shi mai bada labarin motarsu tana baya tare da na 'yan sanda. Su ma da hare-harben suka yi yawa wadanda suke baya su ma sun yi ta kare.
Saidai wadanda suka gudu sun isa inda sojoji suke sun kuma shaidawa sojojin abun da ya faru. Sarkin Askira ya fada ma sojojin su je wurin da lamarin ya faru amma sai suka ce ba zasu je ba domin basu tambayi babbansu ba.
Daga bisani su wadanda suka kai kuka wurin sojojin sun koma inda lamarin ya faru nan suka sami gawar sarkin Gwoza Alhaji Shehu Idris Timta da na 'yansanda guda biyu. An harbi sarkin a wuya da hakarkarinsa.
Duk wadanda aka zanta dasu sun shaida sarkin a matsayin mutum mai kyakyawan halaye da shugabanci na gari.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.