Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Sun Sha da Kyar daga Boko Haram


Ijabula Seltimari daga Izghe daya daga ikin wadanda suka sha da kyar a hannun 'yan Boko Haram a garin Izghe, jihar Borno.
Ijabula Seltimari daga Izghe daya daga ikin wadanda suka sha da kyar a hannun 'yan Boko Haram a garin Izghe, jihar Borno.

Wakilin Muryar Amurka ya samu wasu da suka sha da kyar a hannun 'yan Boko Haram yayin da suka kai hari a garin Izghe inda suka kashe 'yan uwan Ijabula da kakansa da wasu.

Wakilin Muryar Amurka ya cigaba da zantawa da 'yanuwan Ijabula Seltima wanda ya tsallake rijiya da baya yayin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai hari a garin Izghe wanda suka yi kaca-kaca da shi da hallaka mutane da dama. Garin gaba daya 'yan kungiyar Boko Haram sun koneshi.

Wannan mata tace yayin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai hari a wata anguwar Maiduguri inda suke da zama sun kone gidajensu lamarin da yasa suka gudu suka koma kayensu kusa da Izghe. Nan ma basu tsira ba.

Basu dade da komawa kauyensu ba sai 'yan Boko Haram suka kai hari. Sun shiga gidan danuwan maigidanta da shi Ijabula wanda shi ma danuwan maigidanta ne. Idan ba'a manta ba shi Ijabula ya sha harbi da asarar dukiya da 'yanuwa.

Matar tace bayan sun gama da 'yanuwan maigidanta, wato sun kasheshi da kakansa da matar da wasu sai suka dawo kanta suna neman maigidanta. Bayan sun bincika basu ganshi ba sai suka kwace 'yan kudin da take dashi. Har sun tafi sai suka dawo suka ce ta basu ashana. Da ashanar suka kone motar Ijabula kanin maigidanta da duk ababen hawa da suka tarar tare da gidaje.

Ga firar da suka yi.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00
Shiga Kai Tsaye




.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG