Biyo bayan kawar da umurnin kwamishanan 'yansandan Abuja da babban sifetonsu yayi kungiyoyin dake zaman durshen a Abuja akan dalibai mata da kungiyar Boko Haram ke cigaba da yin garkuwa dasu, sun koma yin zaman durshen matsawa gwamnati har sai an ceto yaran.
'Yan zanga-zangar sun koma dandalin Unity Fontain dake Abuja.Tun farko masu zanga -zangar sun ci karo da masu adawa da zaman durshen din.
Shin me yasa suka dage da cigaba da zaman durshen bayan 'yansanda sun ce su dakata sai lamuran tsaro sun inganta. Wani Kabiru Sani Bello dake kan gaba a zaman durshen yace babban kukansu shi ne suna son gwamnati ta mayarda hankali akan maganar ceto yaran da ake garkuwa dasu. Sace yaran yace zai kara kawo koma baya ga harkokin ilimi, musamman na mata a arewacin kasar.Sani Bello yace ba zasu daina zaman durshen ba sai ranar da suka ji yaran sun fito lafiya lau. Yakamata gwamnati ta tattauna da 'yan kungiyar Boko Haram kamar yadda Amurka tayi da 'yan Taliban akan sojansu daya da yin musaya da 'yan Taliban biyar. Yakamata gwamnati ta zauna da 'yan Boko Haram su tsara yadda za'a fito da yaran.
Dauda Iliya dan asalin Chibok yana cikin masu zaman durshen din. Yace labaran da suke samu basu da dadi. Kullum ana jin yadda suke farma kauyu kauyuka suna kashe mutane.Makonni biyu da suka wuce sun farma kauyuka sun fi bakwai a lardin Chibok. Yanzu sun sake komawa wajen Gwoza sun tarwatsa wasu kauyuka.
Ita kuma Aishatu Yusuf ta nuna damuwa da yadda gwamnatin Borno ke tafiyar da lamuran 'yan matan da suka kubuce daga cikin wadanda aka sace. Tace an debosu wai su je su rubuta jarabawa. Yadda suke yanzu ba batun jarabawa ya damesu ba. Abun da suke bukata shi ne kula da lafiyar jikinsu da zuciyarsu. Yakamata gwamnati ta basu tabbacin cewa abun da ya samesu ba zai kara faruwa ba.
Ga rahoton Saleh Ashaka.