Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane 31 A Pakistan


Hari Kunar Bakin Wake A Quetta A Pakistan
Hari Kunar Bakin Wake A Quetta A Pakistan

An kashe akalla mutane 31 kana wasu 40 sun jikata a wata fashewa, a runfar zabe a kudu maso yammacin Pakistan a yau Laraba, bayan wasu sa’o’i da fara kada kuri’ar zaben wakilan majalisar dokoki.

Wani babban jami’in yan sanda ya fadawa Muryar Amurka dan kunar bakin waken ya kaiwa wani taron jama’a da suke rumfar zabe a Quetta hari ne a kan babur.

Wadanda harin ya shafa sun hada ne da masu kada kuri’a da yan sanda da wakilan yan siyasa.

Akber Khan ya kada kuri’arsa a rumfar zaben kuma ya shedi lamarin.

Yace na kada kuri’a ta a rumfar zaben. Ina jin gajiya a jikina sai na koma shago na samu abin sha mai sanyi, bayan haka ina fita a gaban shago sai na kasa tafiya yayin da wannan fashewar ta tashi.

Kungiyar IS mai tsaurin ra’ayin Islama ta dauki alhakin kai harin na yau laraba a garin Quetta, babban birnin gundumar Baluchistan, inda aka taba kashe mutane 149 a wurin wani gangamin taron siyasa a watan da ya gabata

Zaben nay au Laraba shine na cikon uku kacal da Pakistan zata canza gwamnati cikin zaman lafiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG