WASHINGTON, D.C. - Cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na kungiyar OIC, Mr. Wajdi Sindi ya sanya wa hannu, babban sakataren kungiyar ta OIC, Mr. Hissein Brahim Taha ya ce bisa kwarewa da basira da Tinubu ke da su, babu shakka zai tafiyar da al’amuran Najeriya domin cimma bukatun ‘yan kasar na kawo ci gaba.
Mr. Hissein Brahim Taha ya jaddada muhimmancin da kungiyar OIC ke bai wa huldarta da Najeriya, sannan ya tabbatarwa da sabon zababben shugaban Najeriyar, kudurin kungiyar OIC na bunkasa dangantaka da hulda da Najeriya ta kowanne fanni, musanan a bangaren bunkasa tattalin arziki da zamantakewa, da kuma yaki da ta’addanci da tsattsaurar akida.
Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen Musulmin ya ta ya Bola Ahmed Tinubu murnar lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar.
Ya kuma yi mu shi fatan samun nasara a ayyukan da ke gabanshi, tare da fatan samun hadin kai da ci gaba a Najeriya.
A ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu ne miliyoyin ‘yan Najeriya suka kada kur’a a zaben shugaban kasa inda aka fafata musanman tsakanin manyan ‘yan takara hudu – Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC, da Atiku Abukabar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour da kuma Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar NNPP.
Hukumar zaben kasar ta sanar da Bola Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara da kuri’u fiye da miliyan takwas.