Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zarge-Zarge Tsakanin Jam’iyyun Siyasa Da Ya Biyo Biyan Zabe A Najeriya


INEC ta ba Tinubu Shaidar lashe zabe
INEC ta ba Tinubu Shaidar lashe zabe

Duk da yake tuni an kaddamar da wasu ‘yan takara da suka sami galaba a zabukan da aka gudanar ranar Assabar a Najeriya.

SOKOTO, NIGERIA - Alamu na nuna abin bai yi wa wasu ‘yan siyasa dadi ba inda suka ci gaba da tayar da jiyojin wuya da zarge-zargen juna tsakanin manyan jam'iyun dake hamayya da juna a wasu jihohi.

Dubban daruruwan masu jefa kuri'a basu sami damar yin zabe a ranar zaben ba saboda wasu dalilai da suka hada da tayar da rigima a runfunan zabe da ake tuhumar ‘yan bangar siyasa da yi a wasu Jihohin Najeriya, lamarin da yasa aka yi watsi da sakamakon zaben a dubban runfunoni.

A jihar Sokoto jam'iyyar PDP mai mulki da babbar jam'iyar adawa ta APC suna nunawa juna yatsa akan zargin tayar da rigima a lokacin zaben wanda ya haifar da soke wasu runfunan zabe wanda hakan ya sa babu mai murna da zaben.

Rigingimu a lokacin zaben a jihar Sokoton sun sa an kasa ayyana ko daya daga cikin ‘yan takarar majalisar dattawa a zaman wanda ya lashe zabe a dukkan mazabu 3 na jihar, da kuma da yawa daga cikin ‘yan majalisar wakilai, abinda ya haifar da zarge-zarge da tayar da jiyojin wuya tsakanin Jam'iyun APC da PDP, inda jam'iyar ta PDP ta fara kokawa kamar yadda shugaban ta na jiha Bello Aliyu Goronyo ya shedawa manema Labarai.

Ita kuwa jam'iyyar APC ta bakin shugaban ta Isa Sadiq Achida ta ce PDP kawai tayi saurin kokawa ne amma ai itace mai laifi.

Haka kuma Jam'iyar ta PDP a wani taro da ta gudanar ta ce ta dauki matakin hana sake faruwar cin mutunci da ta ce an yi mata, har gwamnan Jihar Aminu Waziri Tambuwal ke shedawa jama'a cewa a fito ayi zabe kuma a hana duk mai son tayar da rigima.

Tun kafin zabubukan sai dai rundunar 'yan sandan jihar ta yiwa ‘yan siyasa gargadin gujewa duk wani nau'i na tashin hankali, ta bakin mataimakin Babban Sufeto Janar mai kula yankin Arewa maso Yammacin Najeriya Muhammad Hafiz.

Da yake ranar 11 ga wannan watan ne za'a sake fita runfunan zabe, za'a iya cewa wannan ya zama kalubale ga mahukunta su tabbata ‘yan siyasa ba su baiwa Najeriya kunya ba a idanun kasashen duniya.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:

XS
SM
MD
LG