Daga cikin wannan adadi, hukumar ta ce mutane miliyan talatin da bakwai da dubu sittin da dari uku da tasa’in da tara, wato kusan kashi arba’in na masu kada kuri’a a bana matasa ne ‘yan tsakanin shekaru goma sha takwas zuwa talatin da hudu.
Daga cikin matasan, wasunsu wannan shi ne karo na farko da zasu je rumfar zabe don kada kuri'a.
Muryar Amurka ta tattauna da wasunsu don jin ko yaya suke ji kasancewar wannan ne zabe na farko da zasu yi a rayuwarsu.
Khadijah Hussaini Isah, ta ce tana murna sosai don zata zabi wanda take sa ran zai inganta ilimi da samar musu da ayyukan yi.
Ita kuma Bilkisu Usman ta ce ta ji dadin yadda zata shiga sahun ‘yan Najeriya da zasu yanke shawara don ci gaban kasa.
Shi ko Adamu Muhammad Dambam, cewa ya yi ba zai yi zabe ba, saboda ba shi da tabbacin wanda zai zaba shi ne za a ba.
Safiya Abdullahi Ahmad, ta ce zata yi zaben ne saboda samar da wanda zai yi wa 'yan kasa aiki, yayin da Maryam Khalid ta ce tana jin takaicin yadda ba zata kada kuri’a ba saboda matsalar da ta samu wajen rajistar zabe.
Ya zuwa yanzu dai matasan na ci gaba da fadakar da junansu musamman ta kafafen sada zumunta kan muhimmancin yin zabe, yayin da kungiyoyi da daidaikun jama’a ke fadakarwa kan muhimmancin yin gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
Saurari rahoton Zainab Babaji: