Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Kungiyar OIC Ya Fara Ziyarar Aiki A Nijer


Hissein Barhim Taha
Hissein Barhim Taha

Babban sakataren kungiyar kasashen Musulmi wato OIC ya kai ziyara Jamhuriyar Nijer a ci gaba da zagayen kasashen yankin tafkin Chadi da na Sahel da nufin bada gudunmowa wajen nemo bakin zaren game da matsalolin tsaro da na canjin yanayi da suka addabi jama’a.

Makasudun wannan rangadi na magatakardan kungiyar OIC ko OCI Hissein Brahim Taha shine tattaro bukatun kasashen yankin tafkin Chadi da na Sahel domin gabatar da su a taron mahawarar da kungiyar za ta gudanar a ranar 23 ga watan Maris a kasar Pakistan don samar da tallafin da ya dace da halin da ake ciki a wadanan yankuna.

Ambasada Aboubacar Adamou shi ne mai kula da harakokin siyasar kungiyar a nahiyar Afrika kuma a wunin farko na wannan ziyara sakataren kungiyar kasashen Musulmi, ya gana da shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum inda suka tattauna akan batun zaman lafiya.

Ya ce "tare da shugaba Bazoum mun zanta akan batutuwan da suka shafi tsaro da zaman lafiya. Ya kuma jaddada goyon bayan kasarsa ga kungiyar OIC."

"Mun yi magana akan yanayin tabarbarewar sha’anin tsaron da ya biyo bayan halin da kasar Mali ta fada. Saboda haka ya zama wajibi mu tashi tsaye don murkushe matsalolin tsaron da ake fuskanta. Saboda haka a tattaunawar mun fi maida hankali akan batutuwan tsaro da zaman lafiya ta yadda mayaka masu ikirarin jihadi ba za su samu gindin zama ba a wannan yankin."

Sakataren kungiyar ta OIC ya ci gaba da cewa, "Ni da shugaban kasa mun zanta akan halin karancin abincin da aka shiga sanadiyyar fari a damanar da ta gabata. Sanannen abu ne a baki dayan yankin Sahel damana ba ta yi kyau ba. Wannan ya sa zamu tuntubi mambobin kungiyar OIC su taimaka wa kasashen yankin cikin gaggawa.

Bayan ganawa da hukumomin Nijer, Hissein Barhim Taha ya ziyarci jami’ar Musulunci da ke garin Say a jihar Tilabery. Kuma Kafin ya zo wannan kasa, sakataren na OCI ya ziyarci kasashen Chadi da Kamaru. A wannan Talata zai nufi kasar Senegal, sannan zai Karkare wannan rangadi da kasar Gambia kafin ya daga zuwa kasar Pakistan don halartar taron ministocin harakokin wajen kasashe mambobin OIC.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

XS
SM
MD
LG