Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Na Ziyarar Aiki A Nijar 

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Na Ziyarar Aiki A Nijar
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Na Ziyarar Aiki A Nijar

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Jamhuriyar Nijar a yau Alhamis 16 ga watan Maris inda zai tattauna da takwaransa Hassoumi Massaoudou ( Hasumi Masa’udu) kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu masu dadaddiyar huldar diflomasiya.

NIAMEY, NIGER - Amurka da Nijar na matsayin jagororin yaki da ta’addanci a yankin Sahel saboda haka Blinken zai yi amfani da wannan ziyara don tattauna wannan batu a ganawar da zai yi a yammacin yau da shugaba Mohamed Bazoum a fadarsa ba’idin wasu batutuwan da suka shafi tattalin arziki da raya karkara.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Na Ziyarar Aiki A Nijar
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Na Ziyarar Aiki A Nijar

Tsohon ministan tsaro bugu da kari dan majalissar dokokin kasa Kalla Moutari na daukar wannan rangadin na Blinken a matsayin ci gaban da Nijar ke samu a ‘yan shekarun nan a fannin diflomasiya.

Tallafin daruruwan miliyon dola ne Amurka ke bai wa Nijar a kowace shekara don ayyukan raya karkara da suka hada da noma da kiwo da dai sauransu yayinda a wani bangare kasashen biyu suka hada guiwa don yaki da ta’addanci a yankin Sahel.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Na Ziyarar Aiki A Nijar
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Na Ziyarar Aiki A Nijar

Wadanan fannoni na daga cikin na gaba-gaba a jerin abubuwan da za a tattauna a kansu a yayin wannan ziyara ta wuni biyu, wace Honorable Kalla Moutari ke fatan ganin ta kasance wata damar kara karfafa matakai akan batun tsaro.

Nijar na daga cikin kasashen Afrika dake shigar da kaya kasar Amurka ba tare da biyan haraji ba a karkashin tsarin da ake kira la loi AGOA to amma sakataren kungiyar ‘yan kasuwar Import Export Chaibou Tchombiano na kira a sake duba hanyoyin sassauta lamura don ganin harakoki sun kara bunkasa a tsakanin Amurka da kasashe masu tasowa.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Na Ziyarar Aiki A Nijar
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Na Ziyarar Aiki A Nijar

Antoni Blinken wanda ya yada zango a kasar Ethiopia a ziyarar wuni biyu zai ci gaba da rangadinsa ne a nan Nijar har zuwa ranar Juma’a 17 ga watan Maris.

A yammacin yau zasu kira taron manema labarai da takwaransa Hassoumi Massaoudou bayan wata ganawa da shugaban kasa Mohamed Bazoum.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Na Ziyarar Aiki A Nijar .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

XS
SM
MD
LG