Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Blinken Ya Fara Ziyayar Kasashe Uku A Afirka


Antony Blinken, Sakataren Harakokin Wajen Amurka
Antony Blinken, Sakataren Harakokin Wajen Amurka

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Afirka ta Kudu a yau Lahadi, yayin da ya fara ziyarar kasashe uku a nahiyar Afirka.

Baya ga Afirka ta Kudu, Blinken zai ziyarci Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo da kuma Rwanda.

Sakataren zai gabatar da babban jawabi a Afirka ta Kudu a gobe Litinin kan manufofin Amurka game da yankin kudu da hamadar Sahara.

Haka zalika, Blinken zai tabo batutuwan canjin yanayi da kasuwanci da kiwon lafiya da karancin abinci a tattaunawar da zai yi.

A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, ana sa ran sakataren harkokin wajen Amurkan zai yi kokarin rage takun saka dake tsakanin Congo da Rwanda.

Congo ta zargi makwabciyarta Rwanda da goyon bayan kungiyar ‘yan bindiga ta M23, zargin da Kigali ta musanta.

Ziyarar Blinken dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya kammala rangadin da ya yi a Afrika, inda ya kare mamayar da Rasha ta kaddamar akan Ukraine, tare da dora alhakin tashin farashin mai da abinci a Afirka, akan takunkuman da kasashen yamma suka sanyawa Rasha.

Amurka dai ta dora alhakin tashin farashin ne akan yakin da Rasha ta kaddamar a Ukraine.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG