Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken, ya jaddadawa ‘yan Najeriya muhimmacin babban zaben da kasar za ta yi a karshen makon da ke tafe.
A ranar 25 ga watan Fabrairu za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya.
Sai kuma na gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a ranar 11 ga watan Maris.
“Yayin da aka tunkari zabe a Najeriya, wannan wata dama ce ga al’umar kasar da za a saurari ra’ayinsu, ta yadda za su zabawa kasar makoma mai kyau.” Blinken ya ce a wani sakon bidiyo da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar.
Blinken ya kara da cewa, “Amurka na da matukar burin ganin an gudanar da wannan zabe cikin lumana.
“Saboda haka, kuri’arku tana da matukar muhimmanci kamar yadda wannan zabe yake da muhimmanci, ba ga Najeriya kadai ba, har ga ma sauran duniya baki daya.” In Sakataren harkokin wajen na Amurka.
Sakon bidiyion har ila yau na dauke da jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Lisa Thomas-Greenfield wacce ta ce gudanar da sahihin zabe, zai taimaka wajen tabbatuwa ko wanzuwar adalci a kasar.
Kazalika bidiyon na dauke da shugabar hukumar raya kasashe ta USAID, Samantha Powers, wacce ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su ziyarci shafin hukumar zabe ta INEC don ganin sun ilmantu kan yadda za su kada kuri’arsu.
“Amurka ta kasance babbar kawa kuma abokiyar hulda ga al’umar Najeriya.” Blinken ya jaddada.