‘Yan kasashen Mali, Burkina Faso, da kuma Ivory Coast ne su ka fi kwarara wadannan tashoshin mota domin zuwa kasashen Turai.
A hirar shi da Muryar Amurka, Ibrahim Traore, wani yan kasar Mali dake shirin tafiya zuwa Turai yace “na fito daga kasata Mali ne na zo a nan domin na gwada sa’ata, domin ina sha’awar zuwa kasar Italiya ne don na yi aiki wanda zan dogara da kaina har ma na iya na turawa iyaye na wani kaso daga cikin arzikin da na samu a can kuma na san akwai kalubale mai yawa da zan fuskanta a bisa hanya amma duk da haka ba zan karaya ba.”
Ana daukar kowanne mutun guda akan kudi jikka 200 ko 250 na CFA daga Agadas zuwa garin Sabha dake cikin kasar Libiya yayinda direbobi ke mikasu a hannun wasu mutanen da zasu wuce dasu zuwa wata kasar Turai, inji Abdallah Ahmed wanda direba ne dake jigilar bakin haure.
Tsamin dangantaka dake kara kazanta tsakanin Tarayyar Turai da sojojin da suke mulki a Nijar na neman dagula al’amurra inda matasan dake goyan bayan sojoji ke kira ga sabbin mahukuntan Nijar da a soke dokar da tayi wa tattalin arkin kasar matukar illa.
A cikin wata sanarwa da hukumar da ke kula da bakin haure ta fitar, ta bayyana damuwarta akan yadda ake samun kwararar bakin haure zuwa Nijar inda ya bayyana cewa, lamarin na neman subule ma sa idon mahunta.
Saurari rahoton Hamid Mahmoud:
Dandalin Mu Tattauna