Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makomar Bakin Hauren Da Suka Makale A Nijar Bayan Juyin Mulki


Bakin Hauren Da Suka Makale A Nijar Bayan Juyin Mulki
Bakin Hauren Da Suka Makale A Nijar Bayan Juyin Mulki

Kimanin ‘yan Afirka 7,000 da suka yi watsi da niyyar yin kaura zuwa Turai ne suka makale a Nijar tun bayan juyin mulkin da aka yi a watan da ya gabata.

WASHINGTON, D.C. - Dakarun tsaron fadar Shugaban kasar ne suka hambarar da zababben Shugaba Mohamed Bazoum.

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta rufe sararin samaniyar kasar sannan kuma kasashen yankin sun rufe mashigar kan iyakokinsu da kasar a bayan takunkumin karya tattalin arziki da aka sakawa Nijar.

Nijar dai wata muhimmiyar hanya ce da bakin haure ke bi don isa kasar Libya da niyyar tsallakawa tekun Meditareniya zuwa Turai.

John Yambasu mai shekaru 29, bakin haure da ya makale a Nijar bayan Juyin Mulki
John Yambasu mai shekaru 29, bakin haure da ya makale a Nijar bayan Juyin Mulki

John Yambasu mai shekaru 29, wanda ya sauya ra’ayinsa na yin kaura, ‘dan asalin kasar Saliyo ne da ya isa Nijar a watan Yuni, amma jami’an Majalisar Dinkin Duniya suka ce masa sai ya jira an kammala kwashe sauran bakin haure a cibiyar da ake ajiye da su kafin a mayar da shi gida.

Kwatsam, sai wasu ‘yan tawaye suka hambarar da Shugaban kasar ta Nijar bayan ‘yan makonni, lamarin da ya kawo tashin hankali a yankin da kuma rufe iyakokin kasar. Yanzu dai Yambasu ya makale a Nijar

Yana kuma daya daga cikin bakin haure kusan 7,000 da ke kokarin komawa gida a wasu kasashen Afirka da Majalisar Dinkin Duniya ke taimako amma yanzu sun makale a Nijar tun a karshen watan Yuli lokacin da jami'an tsaron fadar Shugaban kasar suka hambarar da zababben Shugaban kasar ta hanyar dimokuradiyya, Mohamad Bazoum.

Bakin Hauren Da Suka Makale A Nijar Bayan Juyin Mulki
Bakin Hauren Da Suka Makale A Nijar Bayan Juyin Mulki

Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun kiyasta kimanin mutane 1,800 a cikin mawuyacin hali irin na Yambasu inda mafi yawamsu ke zaune a kan titunan Nijar saboda cibiyoyin da hukumar kula da ‘yan cirani ta kasa da kasa ke da cunkoson jama’a da ba za su iya daukar fiye da haka ba.

Cibiyoyin suna ɗaukar mutane kusan 5,000 dake kokarin komawa gida.

Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta kasance tana taimaka wa kusan mutane 1,250 a wata suna komawa kasashensu.

Yanzu rufe iyakokin har da ta sama abin da ya tilasta mata dakatar da ayyukanta na maida bakin hauren kasashensu.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG