Iyalai da suka hada da mata masu juna biyu, jarirai da kananan yara yanzu sun makale a yankin iyakar da ke da sojoji, suna jiran taimako.
A ranar Asabar 1 ga watan Yuli, 'yan sanda sun kama bakin haure 48 da masu neman mafaka a wani samame da aka kai wani gida a garin Jbeniana da ke wajen kudancin birnin Sfax. An kai wadanda aka kama cikin dare zuwa kan iyakar kasar Tunisia da Libya, inda suka yi ikirarin cewa jami'an tsaron kasar Tunisiya sun fatattake su karfin tuwo.
Kungiyar ta ce an raba su gida biyu, inda aka fatattake wasu 20 da farko a ranar Lahadi 2 ga watan Yuli. Suna ikirarin tun lokacin da aka kama su 'yan sandan Tunisiya da jami'an tsaron kasar sun sha yi masu duka.
A cikin yan ciranin hadda wata yarinya ‘yar shekara 16 da mata biyu masu juna biyu, wadanda aka bayyana suna cikin mawuyacin hali. Matan sun bayar da rahoton cewa jami’an tsaron Tunusiya sun yi lalata da su.
Hotunan da aka aika wa Muryar Amurka sun nuna cewa sun fasa wayoyinsu na hannu.
Sai dai wasu mutane biyu sun yi nasarar boye wayoyinsu domin yin waya da wani dan fafutuka na kasar Faransa da ke kasar Tunisiya, wanda ya kai kara zuwa ga kungiyoyin kare hakkin bil'adama, ciki hadda da Human Rights Watch.
Mai binciken Hijira na Human Rights Watch, Lauren Seibert, wacce ta tuntubi 'yan gudun hijirar da bakin haure da suka makale a kan iyaka, ta bayyana halin da suke ciki.
“Wannan lamarin na gaggawa ne domin ba wai kawai ana zargin su da zaluntar da dukan da kuma korar karfi da yaji na mutanen da ke tsare ne kawai ba, amma an ajiye su a wani wuri mai matukar hadari.
Seibert ta ce an gaya mata cewa an kuma kori rukuni na biyu na bakin haure 28 da 'yan gudun hijira a yankin kan iyaka da sojoji suke. 'Yan ci-rani sun shaida mata cewa wani matashi ya mutu, saboda da raunukan da ya samu, kuma 'yan ciranin da aka kora su binne shi.
A ranar 4 ga watan Yuli, kimanin mutane 100 da aka kiyasta daga kasashe daban-daban na Afirka ne suka iso. Seibert ta ce bakin haure da ta yi hira da su sun ce an kama wadannan mutanen a Sfax. Mutanen sun hada da masu neman mafaka da aka yi wa rajista, wanda daya daga cikinsu karamin jariri ne da kuma wasu daliban da su ma suke da takardar izinin shiga kasar Tunisia.
Muna da mata masu juna biyu da ke cikin halin kunci. Muna da yara kuma muna da wadanda suka ce kwana daya ko fiye da haka ba su ci abinci ba, da kuma wadanda suka jikkata. Don haka muna kira ga hukumomin Tunisiya da su tabbatar da taimakon wadannan mutanen cikin gaggawa da kuma ba da dama ga duk wasu hukumomin jin kai.”