Hukumar ta shirya taron fahimtar juna tsakaninta da masu muamalar kudi da ita domin sanarda su yadda wannan sabon shirin zai yi aiki. Da yake jawabi a wurin taron shugaban hukumar tashar jiragen ruwan Najeriya Alhaji Habibu Abdullahi yace bayan toshe kurarar kudi ba bisa ka'ida ba haka sabon shirin zai sa harkokin biyan kudi ga hukumar ya kara sauri. Yace yana fata da sabon shirin ya fara aiki biyan kudin da ake yi har na tsawon sati guda ya koma na 'yan mintoci kadan. Yace maimakon mutane suna zuwa ofisoshinsu suna biyan kudi to yanzu zasu biya ne a bankuna kuma da sun biya maimakon su jira har sai kwana uku ko biyar su samu tabbaci sabon tsarin zai sa cikin 'yan mintuna zasu sani.
Kodayake shugaban hukumar yace ana yi masu kwangen kudi amma yace sai sun fara sabon tsarin zasu san irin asarar da suka yi can baya. Amma yace babu shakka akwai kwangen musamman a harkar kasuwanci.
Wani Mr Kehinde Alao dake hulda da hukumar yace sabon tsarin zai rage masu bata lokaci da suke yi wajen biyan kudi kafin su fitar da kayansu daga tashar jiragen. Ban da haka sabon shirin zai rage kashe kudade. Shi ma Malam Nasidi yace sabon tsarin zai rage raguwar sace-sacen kudi da magudi da rage yawan jeka ka dawo.