Hayaniya ta tashi a majalisar wakilai yayin da shugaban marasa rinjaye Samson Osagie ya kawo wani kuduri a kan dakatar da Sanusi Lamido Sanusi a matsayinsa na gwmanan babban bankin.
Matakin da shugaban kasar Najeriya ya dauka shi ne na farko a tarihin babban bankin tun lokacin da aka kafashi sama da shekaru hamsin da suka wuce. Majalisar na ganin cire gwamnan daga kujerarsa yanzu ka iya kawo koma baya ga tattalin arzikin kasar.
A fahimtar Aliyu Gebi dan majalisar wakilan yace cire Sanusi Lamido Sanusi shi ne babban kuskure da shugaban kasar ya taba yi ko kuma da zai yi nan gaba. Yace su ba zasu zauna su rungumi hannuwansu ba bisa ga abun da yayi. Ba zasu yadda ba zasu kalubaleshi.Yace daga majalisa sun nuna ma shugaban kasa cewa bashi da iko ko hurumin yin abun da ya yi. Yace "Tsarin mulkin kasar nan bai bashi dama ba" Ya kara da cewa wadanda suka yi sata can baya sun ce a ciresu amma ba'a ciresu ba sai da Sanusi Lamido Sanusi ya fallasa satar dala biliyan 20 da aka yi aka cireshi.
Sanusi Lamido Sanusi ya dade da zargin ma'akatar man fetur da yin sama da fadi da kudade masu dimbin yawa. Kwana kwanan nan Sanusi ya sake yin zargin an wawure wadansu kudade da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan dubu ashirin. Ya kara da cewa fadar shugaban kasa ce ta bada umurnin biyan tallafi a kan kananzir ba tare da samun amincewar majalisa ba.
Dangane da ko cire Sanusi zai shafi tattalin arzikin kasar Yushau Awalu masani kan tattalin arziki ya yi tsokaci. Yace dama tattalin arzikin Najeriya na fama da matsalar cin hanci da rashawa da rashin iya aiki da basusuka. Kasar ta danganta da lamuni ne daga kasashen da basa bada rance sai sun amince da wasu mutane da suka yadda da su. Idan an cigaba da cire jami'an da suka aminta da su kasar zata sami matsala. Zasu ja baya daga taimakon tattalin arzikin kasar.