Rahotanni na nuni da cewa kusan kashi sittin cikin dari na matasan sun bar sansanin. Daya daga cikin wadanda suka bar wurin horon yace mutane ana gana masu wahala, ana gana masu gwale-gwale. Yace horaswar kamar ta soja take. Yace su sun gaji domin azabar ta yi yawa. Yace horaswar ta wuce misali. Yace abinci ba za'a bari ka ci ba. Kana cin abinci ana razanaka, kana ka sheka da gudu. Yace ko salla ma ba za'a barka ka yi ba.Yace wahalar ta yi yawa su kuma ba aikin soja aka daukesu ba.
Dangane da ko dama basu da masaniyar abun da za'a horas da su sai yace an ce masu akwai aikin sufuri wato yadda ake ba motoci hanya da tsaron unguwanni. Ayyukan suna nan kala-kala amma su basu san abun ba.
To saidai kwamishanan kananan hukumomi da masarautu na jihar Alhaji Abubakar Ahmed Walama ya ziyarci sansanin da ake horas da matasan dake garin Malam Sidi. Yace matsalar yara ce kawai da basu saba da irin horon ba amma zasu cigaba kodayake 'yansandan jihar sun ce basu da labari kan lamarin amma sun tura jami'ansu.
Ga cikakken rahoto.