Irin wadannan 'yan kalaren ne gwamnatin jihar ta yanzu ke son karkata akalarsu ta hanyar horar da su kan sana'o'i daban daban domin dakile tashin hankali tsakanin jama'a da 'yan kalaren ke haddasawa.
Makon jiya ne gwamnatin ta dauki matasa ta kaisu Malam Sidi domin a horar da su. Amma sai gashi wasu da dama cikin yaran sun fice daga sansanin horaswar suna korafin cewa ana yi masu horo mai tsanani irin na soja. Sai dai gwamnatin ta fito ta ce ba gudu ba ja baya. Zata cigaba da horas da matasan domin ta cimma burinta na kawar da 'yankalare daga jihar. Gwamnatin tace bita da kulin da wasu marasa kishin jihar su keyi mata ya jawo hakan, wato matasan tamkar an hura masu kunnuwa ne.
Shugaban ma'aikatan gidan gwamnati Alhaji Ahmed Yayari a wani taron manema labarai da gwamnatin ta kira yace ba gudu ba ja da baya. Horaswar zata cigaba. Ya tunashe da 'yan jarida cewa ranar da aka rantsar da gwamnan ya kira duk matasan dake kiran kansu 'yan kalare da su ajiye makamansu domin ba zai yadda su cigaba ba. Daga lokacin ne yace zai basu horo kan wasu ayyuka ya mayar da su mutanen gari. A karon farko an dauki matasa 1200. Yace a lokacin wasu sun rantse cewa shirin gwamnan na gyara matasan sai sun tabbatar bai ci nasara ba. Na ranar Litinin da gwamnan ya bude shi ne horon kari na biyu inda aka samu matasa 1500 kuma suna Malam Sidi suna karbar horo.
Bayan an soma horaswar sai aka soma samun labarin an kashe yara biyar ko shida a wurin. Alhaji Yayari yace da suka ji haka sun tura kwamishanann matasa da shugabannin hukumomi tara su je su kawo rahoton abun dake faruwa a Malam Sidi. Sun je amma rahoton farko na bogi ne, babu gaskiya a ciki. Kawo yanzu babu wanda aka kashe babu kuma wanda ya mutu.
Gwamnati ta sha alwashin cewa ba zata yadda da 'yankalare ba ko ta halin yaya a jihar. Yakamata matasan jihar su zama mutanen kwarai da hanyar samun abun hannunsu ta hanyar halal
Alhaji Mijinyawa Sani Labaran kwamishanan samarma matasa ayyukan yi yace yaran sun dawo yanzu suna da 1400 kuma duk wanda yake son ya kai ziyara akwai matakan da za'a bi. Sai ofishinsa ya tabbatar ziyarar ta gaskiya ce kafin su bada izini.