Wasu kan kashe kansu da kansu ta hanyar bankadawa kansu wuta ko kuma ratayewa kamar yadda ta faru da wani Sa'idu Babura wanda yake ta'ammali da kwaya yayin da ya sargafe kansa a garin Jalingo.
Bayan ya yi tatila kwayar da ya sha sai ya kama bishiya da igiya ya hau ya sargafe kansa ya fado kasa kafa na lilo. Ba'a farga ba sai bayan sallar asubahi a ka gano gawarsa.
Kwanakin baya ma wani matashi a Jalingo ya sha kwaya kana ya banka ma kansa wuta ya mutu har lahira. Batun ta'ammali da kwaya na kara tayarwa iyaye a Taraba hankali. Wani yace yanzu kana ganin yaro amma kafin 'yan watanni sai a ga yana tafiya can sai ya tube wando kamar ya haukace. Yace abun ya zama gama gari. Gwamnati ta tashi ta taimaka a samu a kiyaye rayuwar matasa.
Wakilin Muryar Amurka ya zagaya wuraren da ake sarafa kwayoyin. Wajen da ake hada hadar kwaya ana kirans tempul ko kuma torabora. Kwayoyin sun hada da turamol da vektra da makamanninsu.
Hukumar dake ta'arnaki da fatauci da shan kwaya ko NDLEA a takaice tace ana samun karuwar masu shan kwaya ajihar Taraba cikinsu ma har da 'yan mata. Alhaji Hassan Abdullahi Zunger kwamandar hukumar a jihar Taraba shi ya tabbatar da ahakan.