Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matan Filato Sun yi Zanga-zangar Bacin Rai


Gwamnan Jihar Filato Jonah Jang
Gwamnan Jihar Filato Jonah Jang

Kasa da mako guda da za'a yi zaben kanana hukumomi a jihar Filato matan unguwar Utan sun yi zanga zangar kin amincewa da yadda gwamnati ke tafiyar hawainiya kan gin hanyar da ta shiga unguwar.

A daidai lokacin da zaben kananan hukumomi ke kara karatowa a jihar Filato alummar jihar sun fara tuhumar gwamnati da kasa cika wasu alkawura da tayi amma ta kasa cikawa.

Kasa da mako guda da za'a yi zaben matan dake unguwar Utan wani bangaren birnin Jos fadar gwamnatin jihar sun fito suna zanga-zangar lumana na nuna bacin ransu kan hanyar da gwamnati ta fara aiki a kai yau shekaru shida kenan amma ta gaza gamata. Matan suna ganin gwamnati ta yi watsi da aikin ne. Matan sun ce barin hanyar yadda take yanzu ya jayo mutuwar wasu, wasu kuma sun kamu da cututuka sanadiyar kurar da hanyar ke tadawa.

Matan dake sanye da bakaken tufafi suna kuma dauke da kwalayen da suka rubuta korafe-korafensu. Wata Maria Gajere tace hanyar ba doguwa ba ce amma yanzu shekara shida ke nan ana abu daya. Tace gwamnati ta zo ta gyara masu hanyar kafin zabe su san da gaske suke yi. Yaransu sun shiga shaye shaye kuma wai kowane gida ya zama inda ake hada wata muguwar kwaya da ake kira goskolo.

Dangane da kare 'ya'yansu Maria tace suna yi masu fada kan shaye-shaye amma zasu kara da bi gida gida suna rushe tukwanen goskolo ko menene ma zai faru. Wata Mary tace suna fama da tari da mura kowane lokaci. Gidan maganin da su mata suka gina bashi da isasshen kayan aiki da magani. Tace tamkar kamar gwamnati ta manta dasu ne. Idan zabe ya zo suna fita su yi amma basu da hanya basu da ruwa kuma basu da asibiti.

Balkisu Abubakar tace sun fito da bakaken kaya su yi kuka ga Allah da kuma gwamnati domin yaran da da basu da ciwon fuka yanzu sun kamu. Tace kura suke ciki kura suke sha kura kuma suke kwanciya da ita. Ciwon fuka na kashe yara.

Kwamishanan gidaje da raya birane Solomon Maren yace gwamnati zata cigaba da hanyoyin da zara majalisar dokokin jihar ta amince da kasafin kudin bana. Ya roki matan Utan su yi hakuri.Dangane da wuraren da gwamnatin jihar bata ba fifiko kwamishanan yace sun maida hankli ne wuraren da ba cunkoso domin a fadada birnin. Wuraren dake da cunkoso sun yi tsarin hanyoyi har ma sun biya diya na nera miliyan dari biyu ma wadanda za'a rushe gidajensu domin yin hanyoyi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:15 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG