ABUJA, NIGERIA - Rundunar ta MNJTF na ci gaba da kai samame inda take cafke abokan burmin ‘yan ta'addan ISWAP da Boko-Haram inda ta cafke ire-iren wadannan mutane masu suna Mohammed Sabo da Sarki Danladi yayin da suke kokarin barin garin Monguno zuwa Tumbuns dake zama tungar ‘yan ta'addan dauke da buhuna, suturu, takardar shaidar kungiyar masu sayar da kifi, da kuma takardar shaidar iya kutsawa har gun ‘yan ta'addan dasu ‘yan ta'addan suka bayar.
Dakarun kazalika sun kuma cafke wasu abokan huldar ‘yan Boko Haram din hanyar jigilar kayayyaki da ta hada Monguno da Kekeno, Cross Kauwa da Baga dauke da kayyaki da zannuwa masu yawan gaske, sannan an sami katin cirar kudi na Banki wato ATM a gun wani mai hulda da ‘yan ta'addan da ake kira Abubakar Usman da kuma jerin ababen bukatu a rubuce da zai sayo wa ‘yan ta'addan ya kai masu.
A wani labarin kuma wasu ‘yan ta'adda wato Bakote Mohammed, Babakura Hala da Banna Modu da suka tsere daga hanun ‘yan Boko Haram sun mika wuya ga sojojin MNJTF shiyya ta uku dake Kijimatari a yankin Monguno inda suka yi bayanin cewa sun daina ta'addancin.
Kazalika suma dakarun tafkin Chadin dake bangaren Nijar dake sintiri sun yi sa'ar cafke wata mota kirar Gulf dauke da man fetur da ba asan me zaiyi da shi ba, kana suka kubutar da wasu mata uku da yaransu kanana da suka ce sun gudo ne daga dajin Sambisa biyo bayan mummunan arangama mai zafi da ake yi tsakanin mayakan Boko Haram da na ISWAP.
Bugu da kari bayan wannan kuma, dakarun sun sake kubutar da wasu Iyalan Boko Haram din 43 da yara kanana 30. Rundunar ta MNJTF ta ce ta lura cikin wata daya da ya gabata an samu karin ‘yan ta'addan dake sulalewa daga Sambisa zuwa tafkin Chadin biyo bayan barin wuta da dakarun kewaya akan ‘yan ta'addan ta sama da kasa.
A kan iyakar Najeriya da Nijar kuwa, yankin kogin Komadugu da Yobe dakarun sun cafke kimanin iyalan mayakan ta'addan su 900 da suka hada da maza da mata, manya da yara cikin wani aiki na soji da hadin gwiwar dakarun kasashe.
Tuni kuma babban kwamandan rundunar Tafkin Chadin ya jinjinawa mayakan tare da neman su kara zage damtse don tabbatar da gaggauta kawo mkarshen ta'addancin, kana ya nemi mazauna yankin tafkin na Chadin da su mara masu baya tare da kai rahoton duk wanda ba a aminta da take-takensa ba.