WASHINGTON, D.C. - An tura rundunar ne a matsayin wani matakin kafa sansanin soji a tsibirin Bouka-Toullorom, tsakanin kauyukan Ngouboua da Kaiga, inda ‘yan Boko Haram suka kai hare-hare da dama a ‘yan shekarun nan.
Sanarwar ta ce 'yan bindiga sun kai hari da sanyin safiyar ranar Talata, inda suka kashe mutane kusan 10 tare da raunata wasu da dama.
Rikicin na Boko Haram da ya barke a yankin arewa maso gabashin Najeriya a shekarar 2009, ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 350,000 tare da tilasta wa miliyoyin mutane barin gidajensu.
Kungiyar Boko Haram ta bazu zuwa yankin tafkin Chadi mai fadama a yammacin kasar, inda sojojin Chadi, Najeriya da Nijar suka kwashe shekaru suna fafatawa da masu kaifin kishin Islama.
Duk da kokarin mayar da su wajen garuruwa, mayakan Boko Haram sun kashe sojojin Chadi 92 tare da raunata wasu 47 a watan Maris din 2020.
Gwamnatin rikon kwarya ta kasar Chadi ta lashi takobin ninka yawan sojojinta nan da karshen shekara ta 2022 domin tunkarar kalubalen tsaro da suka hada da barazanar mayakan Islama da ke da alaka da Al Qaeda da kuma kungiyar IS.
-Reuters