Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Najeriya Ta Gargadi Masu Zanga-zangar Siyasa A Jihar Nasarawa


Masu zanga zanga a jihar Nasarawa da ke Najeriya
Masu zanga zanga a jihar Nasarawa da ke Najeriya

Rundunar sojan Najeriya ta yi Allah wadai da harin tsokana da wasu masu zanga-zangar siyasa su ka kai wa kwamban motocin sintirinta a kan hanyar Lafiya zuwa Makurdi.

Kakakin runudunar sojan Najeriya Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya bayyana cewa, masu zanga-zangar sun rufe babbar hanyar ta Lafiya zuwa Makurdi, a wani mataki na nuna fushinsu bisa hukuncin kotun daukaka kara kan zaben gwamnan jihar, wanda hakan ya janyo dogon layi da cunkoson ababen hawa a kan babbar hanyar ta tarayya.

Rundunar ta ce babban abin bakin ciki shi ne yadda masu zanga-zangar su yi kasadar rufe hanyar kana su ka zo kuma suna zargin cewa sojojin sun kai masu hari.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya Birgediya Janar Nwachukwu ya aikewa Muryar Amurka, ya yi bayani dalla-dalla kan abin da ya faru da kuma hotunan duk abin da ya wakana.

Masu zanga zanga sun fasa gilashin motar sojin Najeriya a jihar Nasarawa
Masu zanga zanga sun fasa gilashin motar sojin Najeriya a jihar Nasarawa

Nwachukwu ya ce sojojin sun kai zuciya nesa, sannan sun nuna kwarewa wajen shawo kan matsalar a tsanake.

Amma duk da haka rundunar sojin ta gargadi masu zanga-zangar da suke yin gangaminsu bisa tsarin doka, tana cewa ba za ta amince da yadda masu zanga-zangar su ka yi ta jifan motocin sojojin ba.

Rundunar sojan ta kuma ja hankalin jama'a da su sani fa cewa tashin hankali ba wata faida da zai haifar, sannan ta ce za ta yi aiki da sauran jami'an tsaro wajen tabbatar da tsare dukiya da rayukan jama'a.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG