Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BORNO: Sojoji Sun Kubutar Da Mutane Da Dama Ciki Har Da Kananan Yara Daga Hannun 'Yan Kungiyar IS


Wasu yara da aka kubutar
Wasu yara da aka kubutar

Jami’an tsaron Najeriya sun ceto mutane da dama da aka yi garkuwa da su galibi mata da kananan yara daga hannun 'yan kungiyar IS masu tsattsauran ra’ayi a yankin arewa maso gabashin kasar mai fama da rikici, in ji rundunar sojan kasar.

Rundunar sojin ta ce da yammacin ranar Litinin ne aka kubutar da mutanen 25 da aka yi garkuwa da su a lokacin da dakarunta suka gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno, yankin da ke fama da tashe-tashen hankula na masu tsattsauran ra'ayi da suka yi sanadin rasa rayuka da kawo cikas ga rayuwar al’ummar yankin tun shekarar 2009, lokacin da mayakan Boko Haram suka kaddamar da hare-haren ta'addanci.

An fara kubutar da 14 daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a ranar Asabar a kauyen Gobara yayin da aka 'yantar da wasu 11 a ranar Lahadin da ta gabata lokacin da sojoji suka kai farmaki maboyar 'yan ta’ddan a kauyen Gava mai tazarar kilomita 130 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno, in ji kakakin rundunar Onyema Nwachukwu.

Sojojin sun fidda hotunan wadanda aka yi garkuwa da su da suka hada da yara kanana. Yawancinsu suna tattare da alamun rashin abinci mai gina jiki kuma suna sanye da tufafin da suka kode, abinda ke nuna cewa ta yuwu sun dade a tsare.

“Dukkan wadanda aka ceto a halin yanzu suna hannun sojojin,” in ji Nwachukwu, yana mai bayyana ayyukan da suka yi a matsayin wani bangare na “kokarin da ake yi na kakkabe ragowar ‘yan ta’addan Boko Haram” a Borno da sauran jihohin Najeriya.

Ya ce wasu ‘yan kungiyar Boko Haram bakwai sun mika wuya ga sojoji ranar Lahadi a wani samame na daban, cikinsu har da manya uku da yara hudu.

Akalla mutane 35,000 ne suka rasa rayukansu yayin da mutane miliyan 2.1 suka rasa muhallansu sakamakon tashe-tashen hankulan na masu tsattsauran ra'ayi da ya bazu zuwa kasashen Kamaru, da Chadi, da Nijar da ke makwabtaka da kasar kamar yadda wasu bayanai daga hukumomin Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya suka nuna.

~ AP ~

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG