Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ce rundunar sojin saman Najeriya ta tabbatar da cewa ta kai hare-haren bam a jihar Zamfara da ke
arewa maso yammacin kasar a ranar Talata. Sai dai kakakin ya ce har yanzu ba zai iya bayar da cikakken bayani kan adadin wadanda aka kashe ba.
Wani jami’in soji ya ce, jiragen yakin sun tare ‘yan bindigar da ke kan babura a kauyen Dan Mani da ke gundumar Sangeko da ke gefen dajin Kuyan Bana inda aka yi musu ruwan bama-bamai.
Wani jami’in da ke cikin aikin ya ce jiragen yaki sun kai farmaki ta sama kan ‘yan bindigar, inda suka kashe – a nasa ra’ayi – kusan 100 da wasu kusan 200 da suka samu munanan raunuka.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce harin da aka kai ta sama shi ne hari na biyu mafi tsanani da aka kai ta sama kan ‘yan bindiga a Zamfara tun shekarar 2015 da sojoji suka daura damarar yakar ‘yan bindigar.
AFP ta ce sun yi kaurin suna wajen yin garkuwa da jama’a daga makarantu da kwalejoji a shekarun baya-bayan nan, suna kakkafa sansanonin a boye a cikin wani katafaren dajin da ya ratsa jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna da Neja.
~ AFP
Dandalin Mu Tattauna