Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Goyi Bayan Yunkurin Matakin Diflomasiyyar Kasashen Afirka ta Yamma Kan Nijar


Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Amurka, yau Talata, ta goyi bayan yunkurin da kasashen yammacin Afirka ke yi na maido da tsarin mulki a Nijar bayan juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga watan Yuli, ta kuma ce matakin diflomasiyya ya fi amfani da karfin soja.

WASHINGTON, D.C. - Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS, na shirin gudanar da wani taro a ranar Alhamis, domin tattaunawa kan rikicin da ke tsakaninsu da gwamnatin mulkin sojan Nijar, wadda ta yi watsi da wa'adin da ya cika ranar 6 ga watan Agusta na maido da hambararren Shugaban kasar, Mohamed Bazoum.

Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS/CEDEAO (Hoto: Facebook/CEDEAO/ECOWAS)
Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS/CEDEAO (Hoto: Facebook/CEDEAO/ECOWAS)

Yiwuwar shiga tsakani da karfin soja zai kasance cikin abubuwan da za su tattauna akai.

“Babu shakka diflomasiyya ita ce hanya mafi dacewa don warware wannan lamarin,” abin da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya shaida wa gidan rediyon Faransa RFI a yau Talata kenan.

A karkashin Bazoum, Nijar ta yi nasarar dakile harin ta'addancin masu da’awar kishin Islama da ya lalata yankin Sahel, kuma ta kasance muhimmiyar kawa ga kasashen Yammacin duniya bayan da wasu makwabtanta guda biyu suka ki amincewa da tsohuwar mai mulkin mallaka, Faransa, inda suka koma ga Rasha.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken

Blinken ya ce Amurka na goyon bayan yunkurin ECOWAS na maido da tsarin mulkin kasar. Sai dai ya ki cewa komai game da makomar sojojin Amurka kimanin 1,100 a Nijar, inda sojojin Faransa da Jamus da Italiya su ma suke.

A ranar Juma’a ne shugabannin kungiyar ECOWAS suka amince da shirin daukar matakin soji, wanda ake kyautata zatan shugabannin kasashen za su yi nazari a kai a taronsu na, Abuja babban birnin Najeriya.

Tawwagar manzonnin kungiyar ECOWAS a karkashin shugabancin Janar Abdulsalam Abubakar da sarkin musulmi Sultan na Sokoto a Nijar
Tawwagar manzonnin kungiyar ECOWAS a karkashin shugabancin Janar Abdulsalam Abubakar da sarkin musulmi Sultan na Sokoto a Nijar

Har ila yau da alama ana ci gaba da kokarin aikewa da wata sabuwar tawaga zuwa birnin Yamai, inda kakakin kungiyar Tarayyar Afirka AU, ya ce Mohamed Ibn Chambas, babban wakilinta na shirin “Silencing the Guns” wato “dakile amfani da karfin soji” ya na cikin tawagar.

ECOWAS ta ki cewa komai.

"Ba za mu amince da daukar matakin soji a Nijar ba, rayuwarmu ta dogara da hakan," in ji Abdoulaye Maiga, kakakin gwamnatin mulkin Mali, wanda ya bayyana haka a gidan talabijin na kasar Nijar.

Mazauna birnin Yamai dai da suka zanta da kamfanin dillancin labaran Reuters na goyon bayan juyin mulkin, inda suka ce hada karfi da karfe da kasashen Mali da Burkina Faso zai karfafa kasashen uku wajen yaki da masu tada kayar baya masu da’awar kishin Islama a yankin.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG