Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar 'Yan Gudun Hijira Ta Duniya: 'Yan Najeriya Na Kokawa Kan Halin Da Suke Ciki


‘Yan gudun hijira daga kasar Sudan
‘Yan gudun hijira daga kasar Sudan

Ranar 20, ga watan Yuni na kowace shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin duba halin da 'yan gudun hijira suke ciki a sassan duniya.

Kasashen Afrika dai na fama da matsalar 'yan gudun hijira a sakamakon yawaitar tashe-tashen hankula da kuma yawaitar yaki ko kuma juyin mulki.

Yara 'Yan Gudun Hijira A Kauyen Luvu da ke Karu A Jihar Nasarawa
Yara 'Yan Gudun Hijira A Kauyen Luvu da ke Karu A Jihar Nasarawa

Yanzu haka dai rahotanni sun nuna dubban jama'a ne ke zaman gudun hijira a kasashen Sudan da kuma yankin Falasdinu a sakamakon yaki da ake gwabzawa a yankunan,

A Najeriya kuma matsalar hare-haren 'yan bindiga ne ke ci gaba da tilastawa jama'a tserewa daga muhallansu, kamar Munnir Mu,azu Ruma daga jihar Katsina mai fama da matsalar 'yan ta'addan daji.

Ya ce halin da 'yan gudun hijira suke a yankunan kananan hukumomi 8 na jihar Katsina abin tayar da hankali ne.

Yan Gudun Hijira a Sansanin Ramin Kura a Sokoto
Yan Gudun Hijira a Sansanin Ramin Kura a Sokoto

Dan Masanin Birnin Gwari Zubairu Abdur'rauf ya ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware akan 'yan gudun hijira ba za ta yi wani tasiri ba sai an hada da daukar matakin kawar da 'yan bindiga da suke tilastawa jama'a barin garuruwansu.

A jihar Neja kuma Muryar Amurka ta zanta da wasu 'yan gudun hijirar dake zaune a yankin Erana ta karamar hukumar Shiroro da suka ce mayakan Boko-Haram ne suka koro su daga garuruwansu na asali.

Hukumomi a fannoni daban-daban na Najeriya sun sha bayyana cewa suna daukar matakai ko dai na kai kayan agaji ko kuma na samar da tsaron da zai mayar da 'yan gudun hijirar muhallansu.

Fata dai shine kyaututuwar tsaro a Najeriya da kuma sauran duniya da kuma magance matsalar yaki a kasashen Afirka da duniya baki daya ta yadda za,a samu kwanciyar hankali gaba daya.

Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:

Ranar 'Yan Gudun Hijira Ta Duniya: Halin Da Na Najeriya Suke Ciki.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG