Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miliyoyin Mutane Na Fuskantar ‘Matsanancin Karancin Abinci’ A Chadi - Kungiyoyi Masu Zaman Kansu


‘Yan gudun hijira daga kasar Sudan
‘Yan gudun hijira daga kasar Sudan

Kimanin mutum miliyan 3 da dubu 400 ne ke bukatar agajin gaggawa a kasar Chadi sakamakon isowar dumbin ‘yan gudun hijirar Sudan da ke gudun hijira.

Wata sanarwa da wata kungiya mai zaman kanta ta kasar Faransa ta fitar mai suna “Action Against Hunger” ta ce, lardunan gabashin kasar Chadi na daga cikin yankunan da ke fama da matsalar karancin abinci a kasar, kuma zuwan 'yan gudun hijirar na kara tsananta bukatun yau da kullum.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ce Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi a cikin watan Maris cewa tallafin abinci ga dubban daruruwan mutanen da ke kwarara daga Sudan zai tsaya a cikin watan Afrilu idan kasashen duniya ba su tallafa ba.

‘Yan Gudun Hijira
‘Yan Gudun Hijira

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci taimakon dala miliyan 242 domin kaucewa bala'i da kuma ci gaba da tallafawa 'yan gudun hijirar Sudan miliyan 1.2. Isar da agajin na da sarkakiya sakamakon damina mai gabatowa da ke barazanar katse hanyoyin shiga gabashin Chadi.

Hukumomin ba da agaji sun ce a halin yanzu tallafin da kasashen duniya ke bayarwa ya shafi kashi 4.5 ne kawai na bukatun da ake da su.

Kasar ta Chadi mai girman gaske, wacce ke tsakiyar Afirka na ɗaya daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya inda mutum miliyan 1.4 da suka fice daga gidajensu a cikin kasar ko kuma daga wasu ƙasashe makwabta. Kimanin mutum 900,000 sun fito ne daga Sudan, inda kusan kashi 90 cikin dari mata ne da yara.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG