WASHINGTON, D. C. - Jirgin ruwan agaji na Turai mai suna Ocean Viking ya hango jirgin tare da mutane 25 a ciki a ranar Laraba. Biyu sun kasance a sume, kuma sojojin Italiya sun kwashe su domin neman musu magani. Sauran 23 na cikin mawuyacin.
Kakakin SOS Mediterranee Francesco Creazzo ya ce dukkan wadanda suka tsira maza ne, 12 daga cikinsu kananan yara ne tare da biyu daga ciki wadanda ba su kai shekara ba. Sun fito ne daga Senegal, Mali da Gambia.
Creazzo ya ce wadanda suka tsira sun ji rauni kuma sun kasa bayar da cikakken bayanin abin da ya faru a lokacin tafiyar. Ƙungiyoyin agaji sukan dogara da bayanan waɗanda suka tsira ne yayin tattara alkaluman matattu da wadanda suka bata a cikin teku, waɗanda ake zaton sun mutu.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane 227 ne suka mutu a kan hanyar tsakiyar tekun Mediterrenean a wannan shekara zuwa ranar 11 ga Maris, ba tare da la’akari da sabon rahoton bacewar da ake kyautata zaton sun mutu ba.
Wannan dai na daga cikin adadin mutane 279 da suka mutu a tekun Bahar Rum tun daga ranar 1 ga watan Janairu. Kimanin mutane 19,562 ne suka isa Italiya ta hanyar amfani da wannan hanyar a cikin wannan lokacin.
Wadanda suka tsira da ransu sun ce jirgin ya taso ne daga garin Zawiya na kasar Libya dauke da mutane 75 da suka hada da wasu mata da kuma karamin yaro daya. Wani inji a jirgin ruwan ne ya karye ‘dan lokaci kadan bayan tashinsu, kuma haka suke ta shawagi kan ruwa.
-AP
Dandalin Mu Tattauna