Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ran da Aka ba Sojoji 80 Hutu a Gwoza, Ranar 'Yan Boko Haram Suka Kai Farmaki


Boko Haram ta kai a Gwoza, 24 ga Agusta, 2014. (File Photo)
Boko Haram ta kai a Gwoza, 24 ga Agusta, 2014. (File Photo)

Wani sojan Najeriya dake bakin daga a kusa da Gwoza, kuma daya daga cikin sojojin da suka tsallaka zuwa Kamaru bayan kazamin fada da 'yan ta'addar Boko Haram.

Wani sojan Najeriya dake bakin daga a kusa da Gwoza, kuma daya daga cikin sojojin da suka tsallaka zuwa Kamaru bayan kazamin fada da 'yan ta'addar Boko Haram, yace rashin kai dauki ma sojojin dake Gwoza, musamman daga manyan bataliyoyin dake Bama da Madagali, yana daya daga cikin dalilan da suka sa 'yan Boko Haram suka kwace garin.

Amma yace babban abin mamaki shi ne, a ranar da aka ba sojoji fiye da 80 dake Gwoza hutun makonni biyu, cikin wannan daren 'yan Boko Haram suka kai farmaki.

Wannan soja da ba ya son a ambaci sunansa yace wani babban dalilin da ya sanya ba su iya kai farmaki kan 'yan Boko haram yadda ya kamata, shi ne manyan makamansu duk tsoffi ne wadanda tun zamanin mulkin mallaka aka kera su, kuma Najeriya ta yi amfani da su a zamanin yakin basasa, da kuma yake-yaken Liberiya da Saliyo.

Yace 'yan Boko Haram sun mallaki sabbin makamai na zamani daga hannun 'yan tawayen Libiya, musamman ma wasu makaman kabo jiragen sama masu aiki da lantarki, wanda yace akwai guda da suka kama dauke da rubutun larabci.

Haka kuma sojan yayi bayanin wasu wurare a bayan Gwoza inda a yanzu 'yan Boko Haram ne suke cikinsu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG