Gwamnan jihar Borno a wata ganawa da yayi da iyayen daliban da aka sace da dalibai hamsin da bakwai da suka kubuta tare da iyayensu ya yi alkawarin samar ma daliban wuraren karatu a wasu jihohin.
Tun lokacin da aka sace daliban wasu batutuwa suka dinga tasowa musamman akan adadin yawan daliban da aka sace da kuma wanda yake da alhakin kulawa da daliban.
Saidai a lokacin dalibai 57 suka samu suka kubuta daga manakisar da 'yan Boko Haram suka shirya masu. Akwai kuma wasu dari da goma sha tara da suka samu arcewa yayin da maharan suka shiga harabar makarantar lamarin da ya taimaka ba'a samu an tafi dasu ba.
Shugaban ma'aikata a fadar gwamnan jihar Alhaji Abu Kyari yace su 57 din suna cikin wadanda aka sace amma suka kubuce. Su 119 kuma arcewa suka yi.
Mr James Yama daya daga cikin iyayen da aka sace 'ya'yansu wadanda har yanzu babu wani takamaiman bayani akan halin da daliban suke ciki. Yace yanzu kusan wata hudu da wani abu babu labarin 'ya'yansu abun na tayarmasu da hankali. Idan an tambayi sojoji ko shugaban kasa sai su ce sun san inda yaran suke. An barsu cikin duhu da rudani. Yanzu suna cikin fargaba domin irin halin da daliban suka shiga musamman labaran da suke samu cewa 'yan Boko Haram na yin anfani dasu wurin kai kunar bakin wake.
Yanzu dai gwamnatin jihar tare da taimakon hukumar dake tallafawa kasashe masu tasowa ta Amurka wato, USAID da wasu kungiyoyi da shugabannin addini suna aiki tukuru su samar ma yaran makarantu.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.