Wani sojan Najeriya dake bakin daga a yaki da kungiyar Boko Haram, yace abubuwan da wani bature dan kasar Australiya ya yi zargi game da cewa akwai hannun tsohon babban hafsan sojan kasa na Najeriya, Janar Azubuike Ihejirika, mai ritaya cikin masu tallafawa kungiyar, akwai kamshin gaskiya, kuma ba manya ne kadai ke da hannu a wannan ba.
Sojan yace su kansu su na kyautata zaton cewa akwai wasu kananan sojan ma a bayan wasu manya, har ma yayi hasashen cewa nan ba da jimawa ba za a ji sunayen wasu.
"Hatta ai a cikin kananan sojoji mu na zargin wadansu a irin wadannan din," in ji shi.
Sojan yace amma su wadannan duka ba zasu iya hana su samun nasarar murkushe Boko Haram ba, idan har ana son su murkushe su.
"Kawai mu abinda muke gani, wannan bature, maganganun da ya fada gaskiya ne. Gaskiya ne wallahi. Ba a son a bari soja suyi fada da Boko Haram ko kadan."