Askarawan sojin saman Najeriya sun kai hari a yankin dake kan iyakokin jihohin Adamawa, Borno da Yobe yankin da 'yan kungiyar Boko Haram suka mamaye har ma suka kafa tutocinsu da sunan daular Islama.
Wasu mazauna yankin Madagali da suka kwana cikin daji sun ce sun kwana suna jin karan harbe-harbe yayin da wasu jiragen yaki suka jefa bamabamai. Amma kuma sun ce sojojin suna jefa bam wuri daban daga inda 'yan Boko Haram suke. Wai suna jefa bam ne akan duwatsu alhali kuwa 'yan Boko Haram suna kan hanya dap da wani ofishin gwamnati. 'Yanbindigan sun tare hanya amma sojojin basu jefa masu bam ba.
Kawo yanzu jama'ar yankin da dama suka arce zuwa kasar Kamaru domin neman mafaka kodayake wasu sun gamu da fushin dakarun tsaron kasar wato jandarmomi. Sojojin Kamaru suna kama mutanen Madagali da sun shiga kasar.
Yanzu al'ummomin yankin na cikin wani halin karancin abinci sabili da dokar hana fita na ba dare ba rana da aka kafa a yankin. Mr. James Abawa shugaban karamar hukumar Madagali ya tabbatar da halin da jama'an ke ciki. Mutane suna neman abinci, magunguna da wajen kwanciya da kuma tsaro. Ya kira gwamnati ta taimaka ta kaiwa mutane abinci.
Farfasa Liman Tukur sakataren gwamnatin jihar Adamawa yace nan ba jimawa ba za'a dage dokar. Sun tuntubi kwamandan sojojin jihar wanda ya bukaci a dan dakata tukunna kafin a dage dokar. Ya ba mutanen Adamawa hakuri da su kara yin hakuri, su dada juriya da taimakon jami'an tsaro.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.