Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Kabilar Eggon da Fulani a Jihar Nasarawa Ya Canza Salo


Gwamna Tanko Al-Makura gwamnan Jihar Nasarawa.
Gwamna Tanko Al-Makura gwamnan Jihar Nasarawa.

Rikici tsakanin kabilar Eggon da Fulani a jihar Nasarawa yanzu ya rikide ya koma na ramuwar gayya inda yanzu yayi sanadin rasa rayuka da kona gidaje.

Kakakin rundunar 'yansandan jihar Nasarawa ASP Umar Ismail Numan ya shaidawa wakiliyar Muryar Amurka yadda lamuran suka faru amma yace komi ya lafa yanzu.

Bayan an kai hari a Agyaragu Tofa da 'yan kabilar Eggon suka yi inda suka kashe mutane biyu suka kuma kona bukokin Fulani goma sha biyar da ginannun gidaje biyar Fulani kuma suka kai ramako. Sun kone gidaje fiye da arba'in da shida.

Da dare mutanen kabilar Eggon sun shiga Asakyo sun kone wasu gidaje dake kusa da gidan sarkin garin tare da fasa gidan sarkin. Kawo yanzu babu gawar da 'yan sanda suka gani.

Jiya kuma an sake samun barkewar rikici a Tudun Adabu. Nan ma Fulani ne suka kaiwa kabilar Eggon hari. An kone gidaje kimanin guda arba'in an kuma gano gawarwakin mutane. Yanzu dai kura ta lafa a garin.

Wani mutumin kabilar Eggon Alhaji Ahmadu daga Tudun Adamu yace da safe ne suka ga mutane dauke da bindigogi suna harbe-harbe kafin su ankara sun ga Fulani ne zalla. Sun gudu Fulanin kuma sun bisu da harbi. Ya nuna gawarwaki kamar guda takwas har da na dan'uwansa.

Shi kuma Jabar Usman sakataren Miyetti Allah a jihar Nasarawa yace wadanda suka kai harin ba Fulani ba ne. Yace su da aka kaiwa hari a wasu wurare yanzu suna Dunama a cikin garin Lafiya inda suka samu mafaka. Kana yaransu suna wurin shanu. Maganar Fulani sun kai hari yace shi bashi da labari. Kawo yanzu duk wadanda rikicin ya shafa Fulani da Eggon da wasu kabilu gwamnan jihar Nasrawa ya shirya ana basu abinci da wurin sa kai.

Yadda za'a magance matsalar ita ce manyan kabilar Eggon da na Fulani da jami'an gwamnati su zauna a tattauna.

Shi ma Daniel shugaban matasan Eggon yace jami'an tsaro sun yi kokari su hana Fulani shiga Tudun Adabu amma abun ya cutura dalili kenan da aka samu mummmunan rikici a wurin. Yace shi bai san abun da ya hadasu da Fulani ba domin shi da shugaban matasan Fulani tare da kwamishanan 'yansandan jihar da na 'yansandan ciki wato SSS sun tattauna kuma sun dauki mataki da su zasu je wurin mutanensu kana Fulani su je wurin nasu. Suna gama magana washe gari sai suka ji Fulani sun shiga wani kauye.

Ga rahoton Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG