Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yanbindiga da Jami'an Tsaro Sun Fafata a Bauchi


Wasu sojojin Najeriya.
Wasu sojojin Najeriya.

Al'ummomin unguwar Wuntin Dada dake kusa da Bauchi jiya sun tashi cikin fargaba da tsoro sailin da wasu 'yanbindiga da kuma jami'an tsaro suka dinga harbe-harbe tsakaninsu har na tsawon mintuna arba'in.

Mazauna unguwar sun shaidawa Muryar Amurka cewa 'yanbindigan suna cikin mota ne suka ratsa cikin unguwar suka nufi inda sojoji suke kula da shige da ficin jama'a,

Mazaunin unguwar yace sun yi kusan minti arba'in da biyar suna musayar wuta tsakaninsu. Abun mamaki shi ne motar da ta kawo harin ta sa wuta suka nufi cikin gari sun ratsa cikin sojoji da 'yansanda amma basu taresu ba duk da sun bar kofofin motarsu a bude kuma suna rike da bindigogi. Wasu sojojin suna cewa gasu can wasu kuma suna cewa basu ba ne. Suna tsaye mutanen suka wuce.

Har sun kama hanyar Jos sai suka sake dawowa da wasu sojoji kana suka shiga unguwar. A Wuntin Dadan babu wani abu na gwamnati ko wata ma'aikata ko ginin 'yansanda ko na soji. Wai an kashe daya daga cikin maharan maimakon a kamashi domin a san abun da ya kawosu unguwar.

Wani yace sun tashi ke nan daga masallaci sai suka soma jin harbe-harben da suka rikitar dasu. Dole suka shige gidajensu suka kulle. Bayan kura ta lafa an samu wanda aka harba tare da motar da suka zo da ita. An kara jibge sojoji da 'yansanda a wurin.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammed.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG