Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

RAHOTO NA MUSAMMAN: Shin Katin Zabe Na Iya Hana Magudi? ‘Yan Najeriya Na Kokwanto


Hoton Mai Kada Kuri'a
Hoton Mai Kada Kuri'a

GANJUWA A NAJERIYA - A lokacin da ‘yan Najeriya ke shirin yin babban zaben 28 ga watan Maris na shekarar 2015, martabar zaben ta ta’allaka ne tare da bada karfi akan sabon salon zaben da za’a yi ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa wajen karbar dangwalen duban mutanen kasar.

An kawo na’urar ne don magance magudi da satar kuri’a da cogen katunan zaben da a baya ya gurguntar da zaben shekarar 2011 da har ya haifar da rikicin da aka yi asarar rayukan jama’a. Kwararru suna ganin yiwuwar ma ana iya yin magudin da ya fi na baya idan aka yi la’akari da yadda aka ritsa shugaba Goodluck a kwanar takara da tsohon shugaban kasar a mulkin soja wato Muhammadu Buhari.

Daya daga cikin manazarta yace katin zaben zai taka muhimmiyar rawa wajen yin sahihin zabe amma kuma ba zai hana magudin zabe ba. Duk da yake gwamnatin Jonathan na da burin sanin yanayin sakamakon zaben kafin gama zaben, to amma har zuwa yanzu ba su da kwarin gwiwar cin zaben.

Kamar yadda wani kwararren dan Najeriya Jasper Veen ya fada daga Tsangayar Kimiyyar Dimukuraddiya da Alakar Kasashen Duniya a mai ofishinta a Washington sannan tana samun tallafi daga gwamnatin Amurka da kuma wasu daban. Yace, “ta yaya ake ganin za a iya cimma kare sakamakon saben?”. Veen ya kara da cewa “wannan ita ce babbar tambayar”.

Zargin Magudi Da Rikicin Shekarar 2011

Shekaru hudu da suka shude a lokacin da Buhari da Jonathan suka kara a takarar shugabancin Najeriya, Jonathan din ne ya lashe zaben da kusa kashi 59 daga cikin 100 wanda hakan ya haifar da karon battar da ya shafi addini da bangarancin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 800 sakamakon rashin amincewar magoya bayan Buhari da sukar cewa an yi gagarumin magudi.

A jihohin kasar guda 36 an sami rahotannin cewa an kidaya kuri’un da suka zarce yawan masu kada kuri’ar. An kuma dama lissafin takardun zaben ta hanyar ninninka yawasu fiye da kima duk da dai cewa a haka din zaben na 2011 yafi na shekarar 2007 armashi duk da kurakuran da aka samu. Masu sa idon kasashen turai sun nuna cewa ba zaben bane matsala, amma kidaya kan kuri’un har sun daidaitu shine matsalar.

Duk da ganin kyan dan kyan zaben na 2011 masu sa idon turai din a rahotonsu na karshe sun nuna akwai yiwuwar a yi garambawul akan aiwatar da zabuka a kasar. Kokonton zaben kasar ya ta’allaka ne a rumfunan zabe kididdigar jeka na yi ka ta nuna kashi 13 na ‘yan Najeriya suna da karfin gwiwa aka zabe.

A cikin wadanda basu yarda da shugabanci ba a kasar, kashi 8 ba su yarda da sahihancin zabe ba.an sami sakamakon da ya nuna kuskuren kaso 3 da digo 9 na kididdigar mutum 1000 da aka gwada awon ra’ayoyin a watannin Mayu da Yunin da suka gabata.Wata kididdigar Afrikawa da aka fitar a ranar Talata ta nuna cewa kama daga shugaban kasa, ‘yan majalisun wakilan tarayya da na jihohi da su kansu gwamnonin jihohin sun yi dumu-dumu a sha’anin almundahana da dukiyar kasa.

Katin Zaben Din-Din-Din

A shekarar 2012 ne dai hukumar zaben kasar ta canza da katin da ke aiki da nau’rar kwamfiyuta na din-din-din, shigen irin katinan da ake amfani dasu a bankuna da manyan shagunan saye da sayarwa. Wanda suka fara rabawa mutane sama da miliyan 70 da zasu iya yin zabe sannan za’a yi amfani da na’urori sama da dubu 182 a fadin kasar don tantance sahihanci masu kada kuri’ar.

Nick Dazang ne kakakin hukumar ta INEC ya kuma bayyana cewa, “Amfanin na’urar tantancewar shine ta inganta sahihancin zaben da za a yi. A baya har a wajen zaben ma ake yin magudi da aringizo”. An dai daga zaben daga 14 ga watan Fabrairun da ya gabata kamar yadda suka nuna cewa akwai alamar magudi da kuma son a gama bawa jama’a katunan ne ya sa aka daga di inji Nick.

Kwai zargin da ake wa ‘yan siyasar kasar na sayen katinan zaben don rage yawan masu zaben ko kuma sa su su zabi abinda suke don a rage karfin abokin adawa. Kamar yadda wani daga cikin manyan ma’aikatan INEC din a Bauchi ya fadawa Muryar Amurka. Shi kansa Goodluck ya zargi rashin sahihancin na’urar a watan daya gabata. Sannan wasu ‘yan jam’iyyar mai mulki sun addabi Jegan da yayi murabu amma ya yi burus da su.

Ko a makon da ya gabata an kira shi do ya gana da shugaban kasar. Jegan yace wasu na’urorin suka kasa dauka hoton yatsu amma haka ba zai hana mutum yin zaben ba. Ya kuma tabbatar da cewa, “Ina sake tabbatar muku ni da ma’aikatanmu na INEC zamu yi iyakar kokarinmu na ganin cewa mun yi zabe sahihi kuma marar magudi tare da bawa dukkan ‘yan takara daidaito daga su har jam’iyyunsu.

Rade-Radin Zamba

An yi amfani da harshen turanci da kuma yare na biyu da aka fi magana dashi a kasar wato harshen Hausa wajen yada maganar samun zamba ko magudin katin zaben na din-din-din. Inda aka yi amfani da hanyar shafukan abota ta intanet na tsawon makonni. Shima Clement Nwankwo wani shugaba a Cibiyar Yayata Maganar Shari’a mai zaman kanata da ke Abuja cewa yayi, “Abokan hamayya suna sayen motocin ga magoya bayan dan adawarsu don su kangesu daga marawa nasun baya wajen fitowa zaben.

Wani mazaunin Abuja mai suna Akwei Igono ya sanar da Muryar Amurka cews wani abokinsa na sosai ya sayar da nasa katin zaben a kan naira 1000 (kimanin dalar Amurka 5) ga kawunsa wanda shi kuma kawun nasa ya sayarwa wani dan siyasa akan ninkin wannan kudin da ya saya kamar sau biyar ko goman wannan farashin. Igono yace, “menene hikimar haka?” Ya nuna cewa kokari ne kawai na rage yawan zaben da za’a kara takarar dasu don zabge musu kuri’a.

A Maiduguri arewacin Najeriya ma wani Muhammadu Sani yayi kuka da yadda ake sayen katunan zaben da kananan ‘yan siyasa ke zuwa suna saye akan naira 3000 zuwa 5000 (kimanin dalar Amurka 15 zuwa 25) don hana masu kada kuri’ar su yi zabe. Ana saye ne don rage yawan masu zaben kamar yadda sani ya fahimta ya kuma fadawa Muryar Amurka.

Amma a Adamawa an kama wani mutum dauke da katunan nan zaben har guda 83 a hanyarsa ta zuwa makwabtan jihar ta Adamwa dake arewa maso gabas din Najeriyar. Wanda kuma kakakin ‘yan sandan jihar Malam Abubakar ya tabbatar da cewa mutumin ya fadi cewa zai kai katunan ne can inda ‘yan gudun hijirar boko haram suke amma jami’in tsaron ya nuna yana tababar wannan batu na wanda aka cafke din.

A birnin Legas ma da yafi kowane birni girma a kasar wani mai sanye da kayan sojan ruwa ya kwace katunan wasu ‘yan kasar, kamar yadda wani Mustapha Mohammed mai sana’ar haya da babur din hawa (Achaba) ya bayyana. Ya nuna cewa yana samun kamar naira 5000 (dala Amurka 25) a rana amma sai sojan yace sai ya bashi naira 15,000 (dalar Amurka 75) kafin ya bashi katin nasa.

Da yaki bashi sai ya bashi makullin babur dinsa ya tafi da katin na Mustapha. Yace, “Na yi iya kokarina in karbi katina amma abin ya faskara”. Inji Mohammed dan shekaru 21 dan asalin garin Maiduguri a jihar Borno Ya kara da cewa, “Kawai sun ga alamar ‘yan Arewa zasu zabi Buhari ne shi yasa suke haka”.

Sayarwa Ko Zabe

Wasu ‘yan Najeriyar sun gwammace su sayar da katin da su yi zaben. Isihak Muhammd Lowi dake zaune a kauyen Ganjuwa dake kimanin mil 100 daga arewa maso gabashin birnin tarayya Abuja yace, sakamakon zabukan baya ne yasa bama ya zaton wani abin kirki zai biyo bayn zaben. Saboda haka daga shi har matansa sun tsaida shawarar sayar da katin nasu don samun abin yin jarin saye da sayarwa don hakan ce hanya mafi saukin mallakar jarin a wajensu.

Maganar farashin katin sai ya kada baki yace, “ina son in sayar da katin daga naira 5,000 zuwa 10,000 (dalar Amurka 25 zuwa 50), har matana ma haka. Zan so su sayar su sami na jan jarin saye da sayarwar kamar su itacen girki, magin miya da garin rogo da makamantansu”. Kamar yadda Lowi ya sanar da Muryar Amurka. Ya rufe da cewa, “Hakan ni ina ganin a ra’ayina ya fi zaben da zan yi”.

Rahoton Stein daga Abuja tare da Anne Look a Abuja, sai da Peter Clottey, Jamila Fagge, Bello Galadanchi a Washington da suka taimaka wajen hada wannan rahoton. Sai kuma wadanda suka taimaka da tattaro rahotanni Babangida a Legas da Ibrahim Abdulaziz a Adamawa, da kuma Usman Ahmad Kabara da ya fassara.

XS
SM
MD
LG