Fargabar da aka samu ta yiwuwar sake dage zaben ta ragu inda mataimakin daraktan hulda da jama'a na hukumar zabe ta INEC Nick Dazan ke cewa su sun shirya tsaf.
Nick Dazan yace zasu bude mazabu karfe takwas na safe. Duk wadanda suka bayyana a wurin za'a tantancesu. Bisa ga al'adar arewa masu kada zabe zasu yi layuka biyu, daya na maza daya kuma na mata.
Kowane mai kada kuri'a zai mika katin zabe na din-din-din domin tantancewa. Bayan tantancewar mutane zasu tafi su dawo karfe daya na rana kana su sake layi kuma su kada kuri'a.
Bayan an kammala zabe a kowace mazaba jami'an zabe zasu sanarda sakamakon zaben mazabar. Daga bisani za'a shigar da sakamakon a wata takarda kafin a manna sakamakon a wani bango ko bishiya.
Sakataren SDP Dr. Sadiq Abubakar yayi farin cikin nasarar amincewa da karbar kuri'a koda an jefata a wani akwati daban cikin guda uku.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.