A yau Talata, Vladimir Putin ya karbi rantsuwar kama aikin Shugaban Rasha a karo na 5 a wani biki daya gudana a fadar Kremlin tare da samun karin iko fiye da yadda yake a baya.
A jawabinsa na kama aiki, Putin yace Rasha zata fita daga mawuyacin halin da take ciki a halin yanzu cikin nasara da karin karfi.
Shugaban na Rasha ya kuma sha alwashin tabbatar da “sahihin cigaba mai dorewa da hadin kan kasa da kuma ‘yancinta”.
Putin ya kuma bayyana godiyarsa ga sojojin dake taka rawa a yakin da rasha ta bayyana da “aikin soja na musamman” a Ukraine, fiye da shekaru 2 bayan da aka kaddamar da shi a ranar 24 ga watan febrairun 2022, a bikin da wasu daga cikin sojojin dake fafaftawa suka halarta.
Dandalin Mu Tattauna