WASHINGTON, D. C. - Ziyarar ta Putin ta zo ne a daidai lokacin da Rasha ta kara dogaro da China ta fannin tattalin arziki bayan da Moscow ta mamaye Ukraine sama da shekaru biyu da suka wuce.
A jajibirin ziyarar, Putin ya bayyana a wata hira da ya yi da kafofin yada labaran kasar Sin cewa, fadar Kremlin ta shirya yin shawarwari kan rikicin Ukraine. Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya nakalto Putin yana cewa, "A shirye muke don tattaunawa kan Ukraine, amma dole ne irin wannan tattaunawar ta yi la'akari da muradun dukkan kasashen da ke da hannu a rikicin, kuma ciki har da namu."
Ziyarar ta kwanaki biyu ta shugaban na Rasha na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun kasarsa suka kaddamar da wani farmaki a yankin arewa maso gabashin Ukraine na Kharkiv wanda ya fara a makon da ya gabata a cikin kutse mafi muhimmanci tun bayan da aka fara kai daukin gaggawa, lamarin da ya tilastawa kusan mutane 8,000 barin gidajensu.
Tare da kokarin da Moscow ke yi na dorawa kan nasarorin da ta samu a yankin Donetsk da ke kusa, yakin da aka kwashe shekaru biyu ana yi ya shiga wani mataki mai muhimmanci ga rushewar sojojin Ukraine da ke jiran sabbin kayayyaki na makami da makami mai linzami daga Amurka.
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ce dole ne duk wata tattaunawa ta hada da maido da yankin Ukraine, da janyewar sojojin Rasha, da sakin fursunonin, da kotun hukunta masu laifi, da kuma tabbatar da tsaro ga Ukraine.
-AP
Dandalin Mu Tattauna