Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nasarar Putin Za Ta Hana Mu Komawa Gida - ‘Yan Rasha Da Ukraine


Vladamir Putin
Vladamir Putin

Wadansu 'yan kasar Rasha da Ukraine sun bayyana nasarar zaben Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a karo na shida a matsayin koma baya, yayin da kasashen yammacin duniya ke Allah wadai da zaben.

A birnin Bonn na tarayyar Jamus, daruruwan ‘yan Rashan da suka nemi mafaka sun yini cikin alhini. A cikin hirar ta da Muryar Amurka, Shugabar wata kungiyar daliban da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, damuwarsu ita ce tasirin nasarar Putin kan fadansa da Ukraine.

‘’Ina da yakinin cewa, bayan sake zaben Putin, dangantakar Rasha da Ukraine za ta kara tabarbarewa, kuma yakin zai ci gaba ne kawai, kuma fararen hula za su ci gaba da mutuwa. Yakin zai zama na rashin imani da ma'ana."

Su kuwa ‘yan Ukraine da ke da fatan ganin sun koma kasarsu nan bada jimawa ba, idan har an samu sauyin gwamnati da za ta dakatar da fadan, murna ce ta koma ciki.

A nata bayanin, wata daliba mai suna Maria Olga ta ce, ta kadu da jin labarin nasarar Putin a radiyon Jamus. "Na jima ina mamaki ina tambayar kaina ya aka yi haka ace mutum guda ya dawama kan mulki duk da ba dadin shugabancinsa ake ji ba, yanzu ba zan ga çıkan burina na ganin an kawo karshen rikicin har in koma gida ba’’

Ga wasu daga cikin daliban da rikicin ya katsewa karatu da ala dole suka tsere daga Ukrainę kamar Hernandez, ya ce, ‘’ba shiri na bar Ukraine nayi ta fatan ganin an kawo karshen rikicin doń na koma na kamalla karatu na, yanzu sai yadda hali yayi’’

Zarge-zarge na rashin adalci saboda matakin gwamnatin Shugaba Putin na garkame abokan hamayya a gidan yari don hana su shiga takara da kuma batun tauye ‘yanci sun dabaibaye zaben na Rasha da sakamakonsa ya bai wa Shugaba Vladimir Putin mai shekaru 71 wa’adin mulki a karo na biyar

Saurari rahoton Ramatu Garba:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG