Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paparoma Francis zai gana da Hafsan Hafsoshin kasar Myanmar


Paparoma Francis
Paparoma Francis

Ganawar da Paparoma Francis zai yi da Hafsan Hafsoshin Myanmar nada nasaba da zargin cin zarafin kabilar Royhingya wadanda Musulmai ne a jihar Rokhine da aka ce sojojin kasar sun yi masu kisan kare dangi

A halin da ake ciki kuma, Paparoma Francis zai gana da Hafsan Hafsoshin kasar Myanmar da kuma al’ummar Musulmin Rohingya, wadanda ke zargin sojojin kasar da kuntata masu.

Yayin wannan ziyarar da zai kai kasar ta Myanmar daga ranar 26 ga wannan wata na Nuwamba, Paparoman zai gana da Hafsan Hafsoshin soji Janar Min Aung Hlaing dab da lokacin da zai wuce zuwa kasar Bangladesh mai makwabtaka da Myanmar din.

Kungiyoyin rajin kare hakkin dan dam da MDD na zargin sojojin kasar Myanmar da nuna rashin Imani ga al’ummar Musulmi tsiraru.

MDD ta yi kiyasin cewa Musulmin Rohingya fiye da 600,000 ne su ka gudu zuwa Bangladesh, inda su ke zaune cikin wani yanayin ban takaici, a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Paparoma zai gana da wasu daga cikin ‘yan gudun hijiran idan ya isa Bangladesh daga ran 1 ga watan Disamba.

“Ziyarar ta Paparoma na zuwa ne a wani muhimmin lokaci ga kasashen biyu.” A cewar mai magana da yawun Fadar Paparoman Greg Burke, wanda ya kara da cewa ya na ganin ziyarar za ta yi ma’ana.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG