Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

VATICAN: Ana Tuhumar Wani Limamin Katolika Da Laifin fyade


Pope Franncis
Pope Franncis

Ana tuhumar wani limamin darikar Katolika da laifin fyade. Cardinal George Pell, shine limamin katolika mafi girma da aka taba gurfanarwa gaban kotu da aikata wannan laifin.

Wani limami dan kasar Australia, George Pell, daya daga cikin manyan jami’an fadar Vertican kuma babban mashawarcin Paparoma Francis, ya bayyana karon farko a wata kotun kasar Australia inda ake tuhumarsa da laifin fyade.
Limamin dan shekaru saba’in da shida bai ce komi ba a lokacin da ake gabatar da karar a kotun dake Melbourne yau Laraba, inda aka bada karfi kan tsarin sharia. An tuhume shi da aikata laifukan fyade da suka shafi mutane da dama a shekarun baya.

Lauyan Pell, Robert Richter ya shaidawa kotun cewa, wanda yake karewa ba zai amsa laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa ba, ko da yake ba a bukatar ya yi haka a zaman na yau.
Pell wanda yake matsayin jami’in kudin fadar Vetican tun shekara ta dubu biyu da goma sha hudu,shine jami’in darikar Katolika mafi girma da aka tuhuma da aika laifin fyade a jerin irin wadannan abin fallasar da aka jima ana zargin limaman darikar a kai.
Paparoma Francis ya amince da ba Pell lokaci domin ya koma Australia ya kare kansa daga zargin, sai dai bai sauke Pell daga mukaminsa ba.
An jima ana zargin Pell da gaza daukar mataki kan limamai da ake zargi da cin zarafin kananan yara ta fuskar fyade a lokacin yana babban limamin Melbourne da Sydney.
Zai sake bayyana gaban kotun ranar shida ga watan Oktoba.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG