Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Rajin Kare Hakkin Bil'adama Sun Caccaki Papa Roama Francis


Masu rajin kare hakkin Bil'adama sun caccaki Papa Roma Francis saboda kin yin magana akan 'yan kabilar Rohingya masu yawan Musulmai da yayi.

Papa Roma Francis, ya isa Bangladesh, bayan ziyarar kwanaki hudu da ya kai a makwabciyarta Myanmar, inda yaki ya fito a bainar jama'a yayi magana kan matsalar 'yan gudun hijira na Musulmi 'yan kabilar Rohyingya.

Yau Alhamis ne papa Roma ya bar Mynamar, bayan da ya halarci wani gangami na addu'o'i tare da mazauna kasar mabiya darikar Catholic, a birnin Yangon, birni mafi girma a kasar kuma tsohon babban birnin kasar.

Masu rajin kare hakkin Bil'adama sun caccaki Papa Roman, saboda bai yi magana kai tsaye kan rikicin na 'yan Rohyinga ba, tsiraru da aka hana 'yancin walwala a kasar da mafi yawan al'umarta mabiya addinin Budha ne, wadanda suke kallon su a zaman 'yan ci rani daga Bangladesh, duk da cewa iyalai masu yawa suna kasar na tsawon kaka-da kakanni.

Lamarin ya kara tsanani tun cikin watan Agusta, lokacin da sojojin kasar suka kaddamar da farmaki kan kauyukan 'yan Rohyinga, a jahar Rakhine, a zaman martani kan harin da mayakan sakan kabilar suka kai kan jami'an tsaro.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG