Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta yi amfani da dabarun nasarar ta a zaben Edo a zaben gwamnan jihar Ondo da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba.
Shugaban kuma ya kara da cewa za a yi amfani da wannan tsari a zabukan da za a yi nan gaba a Anambra da sauran jihohin Kudu maso Gabas.
Da yake magana a ranar Litinin a Abuja yayin bikin nasarar zababben gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebolo tare da mambobin jam’iyyar na jihar Edo Ganduje ya jaddada muhimmancin jam’iyyar APC ta kara karfi a yankin Kudu maso Gabas.
“Ya kamata babbar jam’iyya kamar APC ta samu cikakken iko a shiyyar Kudu Maso Gabas,” in ji Ganduje, inda ya bukaci shugabannin jam’iyyar da su kara zage damtse don tabbatar da mulkin APC a yankin.
“Mun fara tsara dabarun lashe wasu jihohi. A shekara mai zuwa, muna da burin kwace jihar Anambra. Bari in tunatar da ku cewa muna da wani aiki mai suna ' kusanto da siyasar kudu maso gabas '. Wannan aikin ba manufa ba ce kawai; aiki ne da dole ne a cika shi.
A halin yanzu jam’iyyar APC ce ke rike da jahohi biyu a yankin, amma wannan ya yi kadan ga jam’iyyar da muke da ita. Za mu mai da hankali ne wajen fadada isar da mu da kuma dawo da wasu jahohin da za su taimaka mana,” in ji shi.
Bugu da kari, kuma wasu dattawan jam’iyyar APC daga yankin Arewa ta tsakiya karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, Ameh Ebute, sun bayyana kwarin gwiwarsu na ganin zaben 2027 zai kasance tamkar wani aiki mai sauki ga jam’iyyar APC.
Sun bayyana haka ne a lokacin da suka kai ziyara sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja a ranar Litinin don taya Ganduje murna, bisa nasarar da ya samu a babbar kotun da ke kara neman a tsige shi a matsayin shugaban jam’iyyar.
Ebute ya ce, “Muna ganin ya kamata mu zama na farko da za mu zo mu taya ku murnar lashe zaben gwamnan Edo na jam’iyyar; domin kara Edo a jihohin da APC ke iko da su. Ba mu da tantama a kan iyawar ka na jagorancin wannan jam'iyya zuwa wani matsayi mai girma.
“Kuma mun yi farin ciki da aka soke karar da ke neman cire ka a matsayin shugaban jam’iyya. Muna goyon bayan ka kuma za mu ci gaba da ba ka goyon baya don ganin jam’iyyar ta kai ga mataki na gaba. Tare da waɗannan nasarorin, mun yi imanin a shekarar 2027 zamu yi nasara”
Haka zalika, shi ma Ganduje da yake magana kan nasarar da ya samu a babbar kotun tarayya da ke Abuja, Ganduje ya ce,
“Ko shakka babu wannan ikrarin ba shi da tushe balle makama kuma kotu ta dauke shi haka. Ba ma jin tsoron irin wannan kararraki marasa tushe.”
Dandalin Mu Tattauna