Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adawa ga Yunkurin Gwamnatin Najeriya


 Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Gamayyar kungiyoyin malamai dana manyan ma’aikata na sabuwar Jami’ar koyon aikin malinta ta tarayya dake Kano sun bayyana adawar su kan yunkurin Gwamnatin Najeriya na soke daukaka darajar kwalejojin ilimi guda hudu zuwa Jami’o’in koyon aikin malinta da tsohuwar Gwamnatin ta yi gabanin karewar wa’adinta watanni hudu da suka gabata.

Kwalejojin ilimin da tsohowar Gamnatin da ta gabata ta daga likafarsu zuwa Jami’oin koyon aikin malinta sun hada da Kwalejin ilimi ta Zaria, ta Kano ta Owerri da kuma ta Ondo.

Tuni dai aka nada shugabanin ga wadannan jami’oi, baya ga fara tsare tsaren daukar dalibai, gine gine da sauran alamura na jami’oi, da tuni suka kankama.

Bayan kamala wani taron gaggawa gamayyar kungiyoyin malaman da na manyan ma’aikatan sabuwar Jami’ar, kowon aikin malintan ta Kano sun ce akwai wasu tsirarun mutane dake kokarin maida hannau agogo baya game da wannan ci gaba da aka samu.

XS
SM
MD
LG