Wani mutum dan kasar Afirka ta kudu na cike da farin ciki a sakamakon sake ido hudu da yayi da motar sa wadda barayi suka raba shi da ita har na tsawon shekaru dai-dai har ashirin da biyu.
Dan kasuwar mai zama a jahar Pretoria ta Afirka ta kudu mai suna Derick Goosen, ya sami wannan kira mai ban mamaki ne daga wani jami’in dansanda mai suna Kwakwa Ntokola sati biyu da suka gabata dangane da wata mota kirar Toyota kirar shekarar 1988 mai launin toka kamar yadda mujallar Africans Beeld ta ruwaito.
Mutumin da aka sace wa motar mai suna Goosen dai ya bada rahoton sace motar da aka yi masa a shekarar 1993, ana cikin haka ne sai kwatsam ‘yan sanda suka kama wata mota a aikin binciken kan hanya a arewacin lardin Limpopo, amma ko da aka duba an goge lambar dake rubuce a jikin injin motar.
Dan sanda Ntokola ya yi anfani da dabaru daban daban irin nasu har sai da ya gano mai wannan mota wanda ke zaune a jahar Pretoria, kamar yadda jami’in ‘yan sanda Ronel Otta ya fada wa kafar yada labarai ta Reuters.
“wayyo Allah! Zan wanke ta, in shiga in zagaya gari” inji mai motar mr goosen a hirar su da mujallar Afrikaans. Ya kara da cewa “Hmm! Komi na cikin motar na nan kamar yadda yake a da”.