Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddama Kan Matatar Man Dangote


Aliko Dangote
Aliko Dangote

A yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce a game da ingancin man dizal da matatar man Dangote ke fitarwa inda wasu ke ganin akwai masu son ganin bayan kamfanin, hukumar kula da dokokin fannin man fetur ta NMDPRA ta sake jaddada cewa ba haka abin ya ke ba.

Batun ingancin man da matatar man Dangote da wasu kananan matatun mai kamar su Waltersmiths ke Samarwa dai ya samo asali ne jim kadan bayan da shugaban hukumar NMDPRA, Mal. Farouk Ahmad, ya bayyana cewa ingancin man AGO na kamfanonin Dangote da Waltersmiths musamman idan aka duba sinadarin Sulphur a bisa ma’aunin PPM 50 da aka tsarawa kasashen yammacin nahiyar Afrika su rika samarwa, ya yi kasa a PPM 650 zuwa dubu 1.

Lamarin dai na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce inda wasu ke ganin cewa akwai yiyuwar wasu mutane a karkashin kasa a ciki da wajen Najeriya na son ganin bayan matatar man na Dangoten la’akkari da yawan shekarun da aka kwashe ana maganar farfado da matatun man gwamnatin kasar da ya kusan gagara.

Sai kuma zargin zagon kasa daga kamfanonin man kasashen waje don gudun na Dangote ya dauke musu ‘yan kasuwa da ke sayen tataccen mai a wajen su.

Sai dai shugaban hukumar NMDPRA, Mallam Farouk Ahmed ya ce babu kamshin gaskiya a kan batun cewa bangaren gwamnati ke kokarin kushe matatun man kamfanoni masu zaman kansu na kasar.

Ko mene ne masu ruwa da tsaki ke cewa a game da wannan rashin fahimta da ke ci gaba yaduwa, shugaban kungiyar dilallan man fetur ta Najeriya wato IPMAN, Abubakar Maigandi Dakingari, ya ce abin bai musu dadi ba amma kamata ya yi dukkan bangarorin biyu su zauna su fahimci juna.

Tuni dai shugaban matatar man Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya mayar da martani a yayin hira da ya yi da gidan talabijan na Arise a lokacin rangadin aikin gwada ingancin man kamfaninsa.

A cewar Dangote a lokacin da suka fara aiki, ma’aunin ingancinsu na PPM ya kama daga 600 zuwa 650, wanda ya kasance daya daga cikin ma’aunin inganci, kuma a yanayin da ake ciki yanzu suna kan ma’aunin inganci wato PPM 87, yana mai tabbatar da cewa zuwa farkon watan Agusta za su koma PPM 10.

A fannin matakan da ya kamata a bi idan har mutum na son gina matatar mai, Mallam Faruk Ahmad, ya ce akwai matakan ba da lasisi uku da suka hada da na farawa, lasisi na ginawa da kuma lasisin fara aiki.

Yunkurin ji ta bakin matatar man kamfani Dangote a yayin hada wannan rahoton dai ya ci tura, amma dai shugaban kamfanin Dangote ya jaddada cewa man matatar nasu na da inganci kuma yanzu a shirye yake ya sayarwa kamfanin man Najeriya wato NNPCL matatarsa ya huta daga zargin zagon kasa da ake mishi.

Idan ana iya tunawa, an kwashe wasu shekaru matatun man gwamnatin Najeriya kama daga na Fatakwal, Kaduna, da Warri sun daina aikin tace mai, lamarin da ya tilastawa gwamnatin kasar shiga kasashen waje don tace danyen man, wanda ke ci gaba da yin matukar tasiri ga samar da man fetur da kuma daidaita tattalin arzikin kasar.

Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf:

Takaddama Kan Matatar Man Dangote
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG