Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dangote Yana Neman Kafa Bangaren Kasuwanci Ma Matatar Mai Na Legas A London


Aliko Dangote
Aliko Dangote

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote na shirin kafa wata kungiyar hada-hadar man fetur, mai yiwuwa a birnin Landan.

WASHINGTON, D. C. - Mataki ne domin taimakawa wajen samar da danyen mai da kayayyakin da za a samar da sabuwar matatarsa a Najeriya, kamar yadda wasu majiyoyi shida da ke da masaniya kan lamarin suka bayyana.

Kamfanin Mai Na Aliko Dangote
Kamfanin Mai Na Aliko Dangote

Matakin dai zai rage rawar da manyan kamfanonin kasuwanci na duniya ke takawa, wadanda suka shafe watanni suna tattaunawa don samar wa matatar kudade da danyen mai a madadin kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen ketare. Katafariyar matatar mai mai hakar kimanin ganga 650,000 a kowace rana na shirin sake hako mai a duniya kuma ‘yan kasuwa na sa ido sosai kan yadda za ta gudanar da ayyukanta.

Dangote, wanda mujallar Forbes ta kiyasta dukiyarsa a kan dala biliyan 12.7, bai dai bada amsa kan wasu bukatu da yawa ko sharhi ba.

Kamfanonin BP, Trafigura da Vitol da dai sauransu sun gana da Dangote a Legas da Landan a makonnin baya-bayan nan domin bayar da lamuni na kusan dala biliyan uku na aikin da matatar ta ke bukata don siyan danyen mai mai yawa, kamar yadda majiyoyin kasuwanci suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Majiyoyi sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters kuma cewa sabuwar kungiyar ciniki za ta kasance karkashin jagorancin tsohon dan kasuwan Essar Radha Mohan. Wanda ya fara aiki da Dangote a shekarar 2021 a matsayin daraktan samar da kayayyaki da kasuwanci na kasa da kasa, kamar yadda shafin sa na Linkedin ya bayyana. Wasu majiyoyi biyu sun ce tawagar na cikin shirin daukar sabbin ‘yan kasuwa guda biyu.

An dauki kusan shekaru goma kafin a kammala gina matatar man, inda a kashe dalar Amurka biliyan 20, wanda ya zarce da wasu dala biliyan 6 akan kasafin kudin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG